Nunieh: Wike ya shigo ya kubutar da ni bayan ‘Yan Sanda sun shigo mani gida

Nunieh: Wike ya shigo ya kubutar da ni bayan ‘Yan Sanda sun shigo mani gida

Tsohuwar shugabar hukumar NDDC ta kasa, Dr. Joy Nunieh ta bada labarin yadda gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya cece ta bayan jami’an tsaro sun shigo gidanta.

Joy Nunieh ta ce ‘yan sanda sun duro mata cikin gida ne ba tare da takardun bada umarnin cafke ta ba, kuma su ka yi kokarin su buge kofarta, su kama ta.

“Tun karfe 4:00 na safiyar yau, na ji cewa mutane su na kofar gidana, na yi waya, na yi yunkurin tuntubar gwamna domin dama ya fada mani in sanar da shi idan na fuskanci wani abu.”

Nunieh ta ke cewa a lokacin da ta kira wayoyin gwamnan su na kashe, ko da ta tuntubi wasu sai su ka bayyana mata cewa watakila ‘yan sandan karya ne su ka shigo gidan na ta.

“Su ka ce sun zo ne su dauke ni, da na tambaye su ko su na da izni, sai su ka ce babu.”Nunieh da ta yi magana da 'yan sandan.

“Da kimanin karfe 6:00 su ka balla kofar shiga gidan. Can sai Sanata Magnus Abe ya kira ni a waya, ya fada mani ya yi magana da kwamishinan ‘yan sanda, wanda ya shaida masa bai san da zuwansu ba.”

KU KARANTA: Gwamna Wike ya tseratar da Nunieh daga jami'an tsaro

Nunieh: Wike ya shigo ya kubutar da ni bayan ‘Yan Sanda sun shigo mani gida
Joy Nunieh Hoto: Arise
Asali: Facebook

”Sun yi kokarin cafke ni, sai na rufe kofar, na koma daki na. Su ka shigo su ka rika kokarin bude kofar dakina, su ka yi ta fama na kusan sa’a guda, tun da kofar karfe ce.”

Ta ce: “Daga nan sai gwamnana ya zo, ya bukaci takardar iznin cafke ni, kuma ya ji dalilin abin da ya hana su gayyace ni zuwa ofishinsu maimakon su zo kama ni kamar maras gaskiya.”

Tsohuwar jami’ar gwamnatin ta ke cewa yanzu ta zama ‘yar gudun hijira a cikin gidan gwamnatin Ribas.

Dr. Nunieh ta kuma bayyana cewa ta na da shirin zuwa Abuja domin ganawa da kwamitin majalisar wakilan tarayya kafin abin da ya faru yau.

“Wanda ya yi mani barazana ya na gida, wanda ya sace kudin gwamnati ya na gida, mutumin da ya sace takardun ofis ya na gida, wanda ya dauki kudi ya na gida, wanda ya ce mani in yi rantsuwa ya na gida.” inji ta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel