"Za a Dawo a Sake Lale," Sheikh Guruntum Ya Aika Saƙo Mai Zafi ga Turji da Shugabanni
- Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya tunawa Bello Turji da sauran masu aikata ta'addanci cewa akwai wata rayuwar bayan mutuwa
- Fitaccen malamin ya kuma tunawa shugabanni za a gurfana a gaban Allah kuma za a sake lale tun daga farko, kowa zai girbi abin da ya shuka
- Gurumtum ya ce da a ce babu hisabi a lahira da sai a ce babu hikima a tsara rayuwar duniya, sai dai Allah mai hikima ne yana jiran kowa a madakata
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi - Babban malamin addinin musulunci a Arewacin Najeriya, Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya ja hankali kan rayuwar duniya da ta lahira.
Sheikh Guruntum ya tunawa ƴan ta'adda irinsu Bello Turji da azzaluman shugabanni cewa akwai hisabi, akwai ranar da za a tara kowa a sake lale a gaban Allah.

Source: Facebook
Malamin ya yi wannan magana ne a wurin karatunsa na watan Ramadan, kuma Datti Assalafy ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Sheikh Guruntum ya aika saƙo ga Bello Turji
Sheikh Guruntum, wanda Allah ya yi wa baiwa da iya fitar da magana, ya ce da a ce duk kashe-kashen da su Bello Turji ke yi babu wata rayuwa a gaba, da sai a ce babu hikima a rayuwar duniya.
Malam ya ce:
"Yadda ake rayuwar nan ta danniya da zalunci, a ce kuma duk wanda ya yi abin da ya yi, idan ya tafi shikenan ya sha, to ai ba hikima kenan a tsara rayuwar (sai dai ba haka lamarin yake ba)."
"Yanzu yadda su Bello Turji ke kashe jama'a, a ce idan ya tafi shikenan ya sha, haba malam ai an sha da jama'a. Aa ba haka ba ne, za a dawo (ranar Lahira) a sake lale.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Yaran Bello Turji sun sace ɗan Isiyaka Rabiu, matashin ya yi roko a bidiyo
"Za mu haɗu a gaban Allah" - Guruntum
Malaman ya ƙara da cewa ya kamata mutane su hankalta, su gane cewa wannan rayuwar ba komai ba ce, akwai ranar ƙin dillanci, ranar da kowa zai girbi abin da ya shuka.
Sheikh Guruntum ya ce ya kamata ƴan bindiga su gane cewa waɗanda suke zargin sun masu laifi daban, waɗanda su ke kamawa ko su kashe daban kuma duk za a je a haɗu a gaban Allah.
"Duka za mu je gaban Allah, za a tashi ranar gobe ƙiyama, za a tashi, wallahi za a tashi," in ji malamin.

Source: Facebook
Guruntum ya ja hankalin shugabanni
Da yake magana kan shugabanni kuwa, Malam Guruntum ya ce wani haƙƙinsa a jiha ya isa ya samu ilimi, lafiya da walwala mai kyau amma an bar shi yana garari.
"Wani haƙƙinsa a jiha ya isa ya samu ilimi mai kyau, lafiya, walwala da abinci mai kyau, amma an bar shi ya rayu a wulaƙance a tagayyare kuma a ce ta sha?"

Kara karanta wannan
Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda
"Dukiyar da kasar take da shi ya kai a ce talaka ya samu ilimi, abinci, kiwon lafiya, da walwala a rayuwa, duka bai samu ba kuma ka ce wai ta sha? Ba zai yiwu ba, za sake lale tun daga farko (a lahira),"
- Sheikh Ahmad Guruntum.
Malami ya soki rufe makarantu da azumi
A wani labarin, kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Imam Fuad Adeyem ya soki matakin rufe makarantu da wasu gwamnonin Arewa suka yi a watan azumi.
Imam Fuad Adeyemi ya bayyana cewa rufe makarantu saboda azumin Ramadan, ba koyarwar addinin Musulunci ba ce.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
