Gwamna Ya Fara Daukar Ma'aikata, Mutane 2,000 za Su Samu Aiki

Gwamna Ya Fara Daukar Ma'aikata, Mutane 2,000 za Su Samu Aiki

  • Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da daukar sababbin malamai 2,000 domin inganta harkar ilimi da ilimantarwa
  • Kwamishinar ilimi ta jihar, Dr. Halima Muhammad-Bande, ta ce an riga an tantance malamai 391 da suka cancanta a matakin farko
  • An samu jimillar masu neman aiki 18,000, amma 4,000 ne kawai aka tantance, inda sauran jerin sunayen za su fito nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi na shirin kammala daukar sababbin malamai 2,000 a wani yunkuri na kara inganta ilimi a matakin firamare da sakandare.

Kwamishinar ilimi ta jihar, Dr Halima Muhammad-Bande, ta bayyana hakan yayin da take ganawa da manema labarai a Birnin Kebbi.

Jihar Kebbi
Gwamnan Kebbi na daukar malaman makaranta. Kebbi State Government
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa masu ruwa da tsaki a jihar sun ce lamarin zai taimaka wajen bunkasa ilimi.

Kara karanta wannan

Za a kafa babban kamfanin siminti a Arewa, mutane 45,000 za su samu aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Dr Halima Muhammad-Bande, matakin daukar malaman ya biyo bayan kokarin da gwamna Nasir Idris ke yi domin habaka ilimi a jihar.

Matakin farko na daukar aiki a Kebbi

Kwamishinar ilimi ta jihar Kebbi, Dr Halima Muhammad-Bande, ta tabbatar da cewa daga cikin wadanda za a dauka, 391 ne aka zaba a matakin farko.

Ta ce wadannan malamai sun mallaki digiri, HND da kuma takardar kammala karatun digiri na biyu kuma za a tura su makarantu daban-daban a jihar.

Ta kara da cewa za a sake fitar da jerin sunayen wasu malamai da aka dauka, wadanda suka mallaki takardar NCE.

A cewarta, kwamitin daukar aikin malamai ya karbi takardun neman aiki na mutum 18,000, amma 4,000 ne kawai suka samu shiga matakin tantancewa.

Alkawarin cigaba da daukar malamai

Dr Muhammad-Bande ta bukaci sababbin malaman da su jajirce wajen koyar da dalibai domin ci gaban ilimi a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

An fara cike fom domin samun tallafin noman Naira miliyan 1 na Sanata Barau

Vanguard ta wallafa cewa:

"Malami a Kebbi yana da daraja, domin gwamnan jihar mu ma malami ne, wanda ya san muhimmancin ilimi."

Kwamishinar ta tabbatar da cewa wannan shi ne matakin farko na daukar malamai, kuma za a ci gaba da daukar karin malamai domin cike gibin da ake da shi a makarantu.

Ta bukaci wadanda ba su samu nasarar shiga cikin wannan mataki ba da su yi hakuri, domin za a kara daukar sabbin malamai nan gaba.

Shugabannin majalisa sun yaba da lamarin

Shugaban kwamitin ilimi na majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Garba-Bena, ya jinjinawa Gwamna Nasir Idris bisa goyon bayan da ya bayar wajen ganin an samu nasarar shirin.

Muhammad Garba-Bena ya ce:

"Muna farin cikin ganin wannan daukar aiki yana faruwa a lokacin da gwamna malami ne ke rike da mulki.
"Za a ci gaba da daukar malamai har sai an cike dukkan gibin da ke cikin makarantu."

Kara karanta wannan

Talaka zai ci bulus: Gwamna ya bude shagunan sayar da abinci da araha

Shi ma babban sakataren ma’aikatar ilimi, Abubakar Magaji-Nayilwa, ya bukaci sababbin malamai da su jajirce wajen koyarwa domin ci gaban ilimi a jihar da kasa baki daya.

Ya ce gwamnatin jihar Kebbi za ta ci gaba da kokarin inganta rayuwar malamai domin su gudanar da aikinsu cikin jin dadi da kwanciyar hankali.

Malami
Malami na koyarwa a aji. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Facebook

Tinubu zai dauki ma'aikata a jihohi

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin daukar ma'aikata 774 a fadin Najeriya.

Shugaban kasar ya yi alkawari ne ga jami'an lafiya da aka dauka domin aikin sa-ido na wucin gadi a dukkan jihohin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng