Rawanin Wasu Ya Taba Kasa: Sarki Ya Dakatar da Hakimai 67, Sun Shiga Kotu

Rawanin Wasu Ya Taba Kasa: Sarki Ya Dakatar da Hakimai 67, Sun Shiga Kotu

  • Mai martaba Sarkin Benin, Oba Ewuare II, ya dakatar da hakimai 67 daga sarautarsu saboda rashin biyayya ga fada
  • Majalisar gargajiya ta Benin ta bayyana cewa hakiman sun aikata abubuwan da ke nuni da cin fuskar sarki da masarautar
  • Wasu daga cikin wadanda aka dakatar sun kai karar sarkin a kotu, suna cewa ba shi da ikon dakatar da su daga yin hakimci
  • Wannan mataki da aka dauka a jihar Edo ya janyo cece-kuce kan alakar masarauta da tsarin mulkin zamani a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Benin-City, Edo - Majalisar gargajiya ta Benin ta sanar da dakatar da hakimai 67 a masarautar birnin daga mukamansu nan take.

Oba Ewuare II ya tabbatar da sallamar hakiman kan gudanar da wasu ayyuka da suka saba ka'idar masarauta.

Kara karanta wannan

An yi jina jina da 'yan banga suka gwabza kazamin fada da 'yan bindiga

Basarake ya dakatar da hakimai 67 a masarautarsa
Oba na Benin, Ewuare II ya sanar da dakatar da hakimai 67 a nasarautarsa saboda cin amana. Hoto: @jidesanwoolu.
Asali: Twitter

Sakataren majalisar, Frank Irabor, ya fitar da sanarwa a Benin ranar Juma’a, yana mai cewa sun aikata abubuwan da ke nuni da cin fuskar sarki, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya daga darajar Oba na Benin

Hakan na zuwa bayan Gwamna Monday Okpebholo ya daga kimar Oba na Benin, Ewuare II bayan rusa wasu masarautu.

Gwamnatin jihar Edo ta dauki wasu muhimman matakai kan sababbin masarautu da wata cibiyar al'adu da ke jihar Edo.

Wannan na zuwa ne bayan kirkirar sababbin masarautu da tsohuwar gwamnatin Godwin Obaseki ta yi a zamaninta wanda Okpebholo ke ganin ya saba ka'ida.

Menene dalilin dakatar da hakimai 67 a Benin?

Sanarwar ta bayyana cewa Oba Ewuare II ne ya dauki matakin, saboda ayyukan rashin biyayya da adawa da masarautar da hakiman suka aikata.

Ya kara da cewa an hada jerin sunayensu da sanarwar, domin a dauki matakan da suka dace akansu saboda girman laifin da suka aikata wanda ya saba dokokin masarautar.

Kara karanta wannan

Majalisar shari'ar Musulunci ta goyi bayan rufe makarantu, ta kirayi jihohi 3 su bi sahu

Wasu daga cikin wadanda aka dakatar, kamar Farfesa Gregory Akenzua da Edomwonyi Ogiegbaen, sun shigar da kara a kotun Benin.

Fitaccen basarake ya dauki mataki kan wasu hakimai
Hakimai 67 da aka dakatar sun runtuma kotu domin neman hakkinsu. Hoto: @mrexpo.
Asali: Twitter

Korarrun hakimai sun ja layi kan matakin sarki

Dakatattun hakiman sun ce dokar sarakuna da hakimai ta hana sarki dakatar da su, don haka suka kalubalanci matakin a kotu.

Wannan mataki ya janyo tattaunawa kan yadda masarautu ke hulda da gwamnati a tsarin mulki na zamani, cewar rahoton Daily Post.

Rahotanni sun tabbatar da cewa har yanzu ba a san yadda za a warware wannan matsala ba duba da matsayar fitaccen basaraken kan lamarin.

Wannan takaddama mai karfi ta kara fito da rikicin da ke tsakanin tsofaffin al'adu da tsarin mulkin zamani da take jefa tambayoyi kan iyakar ikon sarauta da kuma dokokin zamani.

Oba na Benin ya shawarci matasa kan zanga-zanga

A baya, kun ji cewa Sarkin Benin, Oba Ewaure II ya yi kira ga matasan Najeriya su janye zanga-zangar da suka shirya wanda aka fara a ranar 1 ga watan Agusta, 2024.

Kara karanta wannan

Bayan dakatarwa, majalisa ta dauki wasu matakan ladabtarwa 5 kan Sanata Natasha

A lokacin basaraken ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙara ƙaimi wajen aiwatar da tsare-tsaren da ake sa ran za su share hawayen ƴan Najeriya

Wannan na zuwa ne bayan matasan sun fusata da tsare-tsaren gwamnatin Bola Tinubu wanda ya jefa al'umma cikin mummunan hali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng