Ana tsaka da Rigimar Rufe Makarantu, Shugaban CAN Ya Roki Musulmi a Masallaci

Ana tsaka da Rigimar Rufe Makarantu, Shugaban CAN Ya Roki Musulmi a Masallaci

  • Shugaban kungiyar CAN, Rabaran Daniel Okoh, ya bukaci zaman lafiya tsakanin addinai yayin da ya halarci buda-baki tare da Musulmai a Abuja
  • Okoh ya jinjinawa 'Al-Habibiyya Islamic Society' bisa shirin ciyar da masu azumi 2,300, yana mai cewa hakan na karfafa fahimta da zaman lafiya
  • Ya bayyana cewa Musulmi da Kirista daya suke, yana kira ga ‘yan Najeriya da su fahimci juna domin a samu zaman lafiya da mutunta juna
  • Babban Limamin Al-Habibiyya, Sheikh Fuad Adeyemi, ya ce shirin ciyarwa yana taimakawa mabukata ba tare da la’akari da addininsu ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Rabaran Daniel Okoh, ya bukaci zaman lafiya tsakanin addinai guda biyu.

Daniel Okoh ya fadi haka a jiya Alhamis 6 ga watan Maris, 2025 yayin da ya halarci buda-baki da Musulmai a masallaci a Abuja.

Kara karanta wannan

Yadda rufe makarantu saboda Ramadan a Arewa ya jawo hatsaniya da martani

Shugaban CAN ya bukaci hadin kan Musulmi a Najeriya
Shugaban CAN, Daniel Okoh ya bukaci Musulmi da Kirista su hada kai. Hoto: The Sultanate Council Media Team, Christian Association of Nigeria-CAN.
Source: Facebook

Shugaban CAN ya yi jinjina ga Al-Habibiyya

Okoh ya halarci buda-bakin ne a Masallacin Al-Habibiyya, inda aka ciyar da masu azumi 2,300, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar ya jaddada bukatar hadin kai da zaman lafiya tsakanin addinai guda biyu manya da ake da su a Najeriya.

Ya jinjinawa jagorancin 'Al-Habibiyya Islamic Society' bisa wannan shiri, yana mai cewa irin wannan yunƙuri na karfafa jituwa da fahimtar juna tsakanin addinai.

Okoh ya ce:

“Muna da bambance-bambance, amma ainihi daya muke, dole ne mu nemi hanyar hada kai, na zo nan, kuma zan dawo nan."
Shugaban CAN ya yi buda baki da Musulmi a masallaci
Kungiyar CAN ta roki hadin kan Musulmi domin samun zaman lafiya. Hoto: @presidentofCAN.
Source: Twitter

Shugaban CAN ya shawarci al'ummar Musulmi

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su fahimci addinan juna don a samu mutunta juna da zaman lafiya, ya ce hakan zai kawo fahimta da hadin kai.

Babban Limamin Masallacin Al-Habibiyya, Sheikh Fuad Adeyemi, ya ce shirin ciyarwa yana taimakawa mabukata ba tare da la’akari da addininsu ba.

Kara karanta wannan

'Gwamnonin Arewa wawaye ne': Sowore ya yi kakkausar suka kan rufe makarantu a Ramadan

Ya ce gayyatar sauran kungiyoyin addini da manyan mutane na nufin inganta fahimtar juna da zaman lafiya a Najeriya gaba daya.

Adeyemi ya ce:

“Dole ne mu gane abubuwan da ke hada mu a matsayin Bil’adama da ‘yan kasa, Shi ya sa muke yin abin da muke yi."

An yabawa Al-Habibiyya kan abin alheri ga al'umma

Rahotanni sun zo cewa taron ya samu halartar malaman addinin Musulunci da na Kirista, wakilan kungiyar CAN da sarakuna.

Masu ruwa da tsaki sun ce wannan abin alheri da masallacin ke yi a lokuta da dama zai taimaka wurin tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al'umma.

Kiristoci sun raba abinci ga Musulmai

Kun ji cewa wata coci mai suna Christ Evangelical da ke ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna ta raba hatsi ga al'ummar Musulmi.

Cocin ya raba hatsi ga al'ummar Musulmi mutum 1000 da makarantun Islamiyya domin azumin watan Ramadan da ake ciki.

Babban faston cocin, Yohanna Buru, ya ce sun kwashe fiye da shekara 19 suna gudanar da irin hakan a jihohi biyar na Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.