NNPP: Rikici Ya Ɓalle tsakanin Hadimin Abba Gida Gida da Ɗan Majalisar Kano
- Hadimin gwamnan Kano ya caccaki dan majalisar tarayya Tijjani Abdulkadir Jobe, yana mai cewa dole ne ya yi wa jama’arsa ayyukan da suka dace
- Duk da ba a kai ga sanin abin da ya shiga tsakanin dan majalisar da Sanusi Bature Dawakin Tofa ba, hadimin gwamnan ya yi kakkusan martani
- Sanusi Bature Dawakin Tofa, wanda Darakta Janar ne wajen yada labaran gwamnatin Kano ya ce ya ji Jobe bai yi aikin da ya kamata ba a mazabarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano — Rikici ya sake barkewa tsakanin mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, da dan majalisa mai wakiltar Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado, Tijjani Abdulkadir Jobe.
Hadimin gwamna Abba Kabir Yusuf ya aika sako ga dan majalisar, ya neme shi da ya mayar da hankali kan yi wa jama’ar da suka zabe shi ayyukan da suka dace.

Asali: Facebook
A cikin sakon da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya tunatar da Tijjani Abdulkadir Jobe cewa yana da nauyin sauke hakkokin jama’ar Dawakin Tofa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Jobe ya yi aikinsa a majalisa," Hadimin Abba
Sanusi Bature ya jaddada cewa wajibi ne Tijjani Abdulkadir Jobe ya mayar da hankali kan kawo ayyukan ci gaba domin amfanin jama’ar da suka zabe shi.
Ya ce:
"Mutuncinsa a zauren majalisa shi ne ya gabatar da ayyukan da za su amfani jama’arsa. Dole ne kowanne shugaba ya sauke nauyin da ke kansa, domin akwai hakkin al'umma a wuyansa."
Hadimin gwamna Abba ya caccaki dan majalisa
Sanusi Bature ya yi kakkausan furuci kan Jobe, yana mai cewa ba zai jure cin mutunci ba, ko da ana zaton yana neman takarar kujerar da Jobe ke kai a halin yanzu.

Kara karanta wannan
Zargin lalata: Sanata Natasha na tsaka mai wuya, Hadimin Osinbajo ya tona shirin majalisa

Asali: UGC
Ya ce:
"Kada wani ya dauka wai ina son takara don haka zan juri wulakanci. Ni dan halak ne, kuma na yarda da kaddara. Wallahi, ya fi sauki in hakura da takara in dai ana batun kare mutuncin al’ummarmu."
"Takarar me? Kai ne kake ganin sai da ita zaka rayu? Sai in fasa takarar, kuma in yanke alaka da kai tun da baka da niyyar canja hali."
NNPP: Mun tsawatar kan rikicin hadimin Abba
Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa, ya shaidawa Legit cewa sun lura da sakon da hadimin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa.
Ya bayyana cewa dukkansu matasa ne, kuma ana zargin cewa akwai masu hararar kujerar juna, don haka irin wannan rikici ba abin mamaki ba ne.
Ya ce:
"A mahangar siyasa, wannan ba wani abu ba ne. Tun jiya muka yi masu magana cewa su daina, kuma a matsayinmu na shugabanni, muna da yakinin cewa abubuwa za su lafa."
Gwamna Abba ya dawo da ƴan Kannywood NNPP
A baya, kun ji cewa wasu fitattun mawakan Kannywood da ‘yan wasan barkwanci da suka fice daga Kwankwasiyya sun sake sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP.
Daga cikin waɗanda suka koma akwai Ali Jita, Habu Tabule, Nazifi Asnanic, da Sarkin Waka, bayan sun gana da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnati.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng