Kwana Ya Ƙare: Allah Ya Yi wa Tsohuwar Shugabar Ma'aikata Rasuwa a Watan Azumi
- Tsohuwar shugabar ma'aikatan jihar Kwara, Susan Modupe Oluwole ta riga mu gidan gaskiya tana da shekaru 58 a duniya
- Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yi alhinin wannan rashi tare da miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai, ƴan uwa da abokan arzikinta
- Gwamnan ya bayyana ta a matsayin ma'aikaciyar gwamnati mai gogewa, wacce Allah ya ba ilimi da hikimar gudanar da aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kwara - Tsohuwar shugabar ma’aikatan jihar Kwara, Misis Susan Modupe Oluwole, ta riga mu gidan gaskiya a ranar Laraba tana da shekaru 58 a duniya.
Marigayiyar ta rasu ne kimanin shekara guda bayan ta yi ritaya daga aikin gwamnati na jihar Kwara bisa ga dokar shekarun ritaya.

Asali: Facebook
Gwamna AbdulRazaq ya nuna alhini
Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yi alhinin rasuwar tsohuwar shugabar ma'aikatan gwamnatinsa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana rasuwar Oluwole a matsayin babban rashi ga jihar Kwara da kuma bangaren aikin gwamnati.
Gwamnan ya faɗi haka ne cikin wata sanarwar ta'aziyya da babban sakataren yada labaran gwamnan Kwara, Rafiu Ajakaye, ya fitar a Ilorin, babban birnin Kwara.
Gwamnan AbdulRazaq ya ce marigayiyar shugaba ce mai cikakken ilimi da gogewa a harkar gudanar da aiki.
Ya ce Oluwole ta taka rawar gani sosai, kasancewarta kwararriya mai hazaka, da jajircewa a aiki, kuma ta kasance wacce take da masaniyar yadda ma’aikatan gwamnati ke gudanar da harkokinsu.
Gwamnan ya ce yana alfahari da irin gudunmawar da marigayiyar ta bayar a lokacin da yake aiki tare da ita.
Gwamna ya miƙa sakon ta’aziyya ga iyalanta
Gwamna AbdulRazaq ya mika sakon ta’aziyyarsa ga mijinta, mahaifinta, da duk danginta, tare da ma’aikatan gwamnatin Kwara baki ɗaya.
Ya yi addu’ar Allah ya jikanta, kuma ya bai wa danginta ƙarfin zuciya don jure wannan babban rashi.

Kara karanta wannan
Bayan ƙarewar wa'adin sa'o'i 48, gwamna na neman tattago rigima da Majalisar Dokoki

Asali: Facebook
Tsofaffin ma'aikata sun yi jimamin rasuwarta
Kungiyar tsofaffin manyan sakatarorin na jihar Kwara (ARSPSON) ta bayyana rasuwar Oluwole a matsayin babban rashi.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da shugaban kungiyar, Prince Ayo Fagbemi, da jami’in hulda da jama’a, Alh. Abubakar Mohammed, suka sanyawa hannu.
Tsofaffin ma'aikatan sun bayyana Oluwole a matsayin kwararriyar ma’aikaciya wadda ta bar manyan alamomi da tarihi a fagen gudanar da aiki.
Sun ƙara da cewa tana da kwarewa mai matuƙar amfani, kuma ta kasance jigo a cikin ayyukan gwamnatin jihar da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.
Tsofaffin manyan sakatarorin sun yi addu’a Allah ya jikanta, kuma ya ba wa dangi da duk masu kaunarta haƙurin jure rashinta.
Tsohon hadimin shugaban kasa, Okupe ya rasu
A wani labarin, kun ji cewa rahotanni sun nuja cewa Dr. Doyin Okupe, likita kuma tsohon hadimin shugabannin Najeriya, ya rasu yana da shekara 72 a duniya.
Majiyoyi daga iyalin Dr. Doyin Okupe sun tabbatar da cewa marigayin ya dade yana fama da rashin lafiya kafin rasuwarsa a ranar Juma'a, 7 ga watan Maris, 2025.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng