Wata 5 bayan Tinubu Ya Kore Ta, EFCC Ta Tsare Tsohuwar Minista kan Zargin Kwashe N138m
- Hukumar EFCC tana bincikar tsohuwar ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye, kan zargin karkatar da N138m a shekarar 2023
- EFCC ta na mai zargin cewa Kennedy-Ohanenye ta karkatar da kudin shirin 'P-Bat Cares for Women Initiative' don amfanin kanta da ta ke ofis
- A baya, majalisar wakilai ta gayyaci Kennedy-Ohanenye kan bashin N1.5bn ga kwangiloli, an ce an bayar da kwangilolin ba tare da kasafin kudi ba
- Hukumar ICPC ma tana binciken ofishin ministar kan zargin karkatar da kudi, amma Kennedy-Ohanenye ta musanta dukkan zarge-zargen
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) tana binciken tsohuwar ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye, kan zargin karkatar da N138m.
EFCC ta ce tsohuwar ministar ta saba ka’idojin sayen kaya kuma ta karkatar da miliyoyi yayin rarraba kasafin kudin ma’aikatar na 2023.

Source: Facebook
Yadda Tinubu ya kori Kennedy-Ohanenye daga muƙaminta
Wani jami'in EFCC ya shaidawa jaridar TheCable cewa an tsare Uju Kennedy-Ohanenye a Abuja domin yi mata tambayoyi tun misalin karfe 11 na safe ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kennedy-Ohanenye na daga cikin ministocin da shugaba Tinubu ya sallama a watan Oktobar shekarar 2024.
A Disamba 2024, tsohuwar ministar ta ce ba ta da nadamar ayyukanta ba da kuma jawo ka-ce-na-ce a gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Hukumar EFCC ta tsare tsohuwar ministar mata
Jami'in ya ce yayin binciken an gano yadda wasu kudi na shirin 'P-Bat Cares for Women Initiative' wanda aka karkatar don kashin kanta.
Majiyar ta ce:
“Ana bincike, an gano cewa an karkatar da kudin P-Bat Cares for Women Initiative don amfanin kanta, ba a ba da damar beli ba."
A watan Yuli 2024, kwamitin majalisar wakilai ya gayyaci Kennedy-Ohanenye kan bashin N1.5bn da ake bin ma’aikatar.
Shugabar kwamitin, Kafilat Ogbara, ta ce ma’aikatar ta bayar da kwangiloli ba tare da kasafin kudi ba, kuma an karkatar da kudin.
Ogbata ta ce:
“Ba a biya kudin kwangiloli ba, an karkatar da kudin, saboda haka, ya za a biya kwangilolin nan?”

Source: Facebook
Uju Kennedy-Ohanenye ta magantu kan zarge-zargen
Ogbara ta ce hukumar ICPC ma tana binciken ma’aikatar kan zargin karkatar da makudan kudade da aka neme sama da kasa aka rasa.
A wata hira a ranar 5 ga Yunin shekarar 2024, Ogbara ta ce akwai “korafe-korafe da yawa” kan tsohuwar ministar.
Tsohuwar ministar ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa ba a bincikenta kan karkatar da kudi a cewar Punch.
Hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamnan Akwa Ibom
Mun ba ku labarin cewa hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel.
Emmanuel ya shiga hannun jami'an hukumar ta EFCC kan zargin badaƙalar N700bn a ranar Talata, 4 ga watan Maris din 2025.
Rahotanni sun ce wata ƙungiya ce ta shigar da ƙorafi a kansa game da kuɗin da ya karɓa daga asusun tarayya da yawan basussukan da ya bari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

