Natasha: Matar Tinubu Ta Tsoma Baki kan Zargin Akpabio da Cin Zarafi a Majalisa

Natasha: Matar Tinubu Ta Tsoma Baki kan Zargin Akpabio da Cin Zarafi a Majalisa

  • Uwargidan Shugaban Kasa, Remi Tinubu, ta ce dole a girmama Majalisar Dattawa, tana mai kare ta daga zargin cin zarafin mata da ake yi
  • Remi Tinubu ta ce Majalisar Dattawa ba wurin hayaniya ba ce, tana mai tabbatar da 'yan majalisa na yin abin da ya dace kan batun da ake tuhuma
  • Uwargidan Tinubu ta ce mata su dauki matsayi a shugabanci, ta kuma ce ya kamata su tsaya tsayin daka ka da a rena su ko a ci zarafinsu
  • Yayin da ake shirin bikin Ranar Mata ta Duniya, ta jinjina wa nasarorin da mata suka cimma, tana mai yaba kwazonsu a fannoni daban-daban

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Uwargidan Shugaban Kasa, Remi Tinubu, ta yi magana kan cece-kuce da ake yi a Majalisar Dattawa dangane da zargin cin zarafin mata.

Kara karanta wannan

Zargin lalata: Sanata Natasha ta fitar da saƙo mai zafi bayan dakatar da ita a Majalisa

Remi Tinubu ta ce dole ne a mutunta majalisar, domin tana da kima kuma wuri ne na dattako.

Matar Tinubu ya yabawa majalisa game da lamarin Natasha
Remi Tinubu ta ce majalisar dattawa na da kima bayan zargin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. Hoto: Oluremi Tinubu.
Asali: UGC

Sanatoci sun yi fatali da korafin Natasha

Remi Tinubu ta yi wannan bayani ne yayin da ake zargin Godswill Akpabio, da cin zarafi kamar yadda Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta bayyana, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan fatali da wasu Sanatoci suka yi da kin amincewa da koken Sanata Natasha suna cewa ba a bi ka’idojin majalisa ba, yayin da wasu ke goyon bayanta kan zargin da take yi.

Sanata Tahir Monguno ya ce dokar majalisa ba ta yarda a tattauna batun da ke kotu ba, tun da Natasha da matar Akpabio duk sun kai kara kan lamarin.

Sai dai Sanata Natasha ta musanta cewa ta kai kara kan cin zarafi, ta bukaci Akpabio ya amince da koken nata domin a mika shi ga kwamitin ladabtarwa.

Kara karanta wannan

Ana batun cin zarafin Sanata, Remi Tinubu ta bukaci karin wakilcin mata a majalisa

Remi Tinubu ya magantu kan dambarwar da ke faruwa tsakanin Natasha da Akpabio
Matar Tinubu ta yabawa majalisa game da lamarin da ke faruwa tsakanin Sanata Natasha da Godswill Akpabio. Hoto: The Nigeria Senate.
Asali: Facebook

Zargin Natasha: Remi Tinubu ta goyi bayan majalisa

Da take magana da ‘yan jarida gabanin bikin Ranar Mata ta Duniya, Remi Tinubu ta ce ‘yan majalisa suna yin abin da ya dace.

Ta ce majalisar dattawa ba wurin hayaniya ba ce, dole ne a girmamata duba da kimar da take da shi a kasar.

Remi Tinubu ta ce:

“Majalisa wurin dattako ne, dole a mutunta ta, na yi aiki a can na tsawon shekaru 12, mata su dage ka da a raina su.”

Matar Tinubu ta jinjina wa matan Najeriya bisa jajircewarsu, tana mai yabawa da irin ci gaban da suka samu.

Uwargidan shugaban ta ce matasa ma na da damar yin fice, kamar yadda Zuriel Oduwole ke yi, cewar Channels TV.

Akpabio ya fadi alakarsa da mijin Natasha

Kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya kara yin bayani kan alaƙar da ke tsakaninsa da mijin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Kara karanta wannan

Zargin lalata: Sanata Natasha na tsaka mai wuya, Hadimin Osinbajo ya tona shirin majalisa

Godswill Akpabio ya ce Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan abokinsa ne domin ya halarci bikin aurensa da Sanata Natasha a jihar Kogi.

Akpabio ya tuna da cewa har kwana ya yi a masana'antar simintin Dangote da ke Obajana a jihar Kogi a ranar auren Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.