Yadda Majalisar Dattawa Ta Yi Biris da Rokon Sanata kan Dakatar da Natasha

Yadda Majalisar Dattawa Ta Yi Biris da Rokon Sanata kan Dakatar da Natasha

  • Sanata daga Binuwai ta Kudu, Abba Moro ya roƙi takwarorinsa da su rage wa’adin dakatarwar da aka yi wa Natasha Akpoti-Uduaghan
  • Shugabancin majalisar dattawa ya umarci kada ƙuri’a kan shawarar da Kwamitin ladabtarwa na Majalisa ya gabatar a kan Sanata Natasha
  • Moro ya bayyana cewa kodayake Natasha ta saba dokokin majalisa, kamata ya yi a bi ta da sassauci, kamar yadda ake bin yara masu taurin kai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaMai wakiltar yankin Binuwai ta Kudu a majalisar dattawa, Abba Moro, ya roƙi majalisar da ta sassauta dakatarwar da aka yi Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Ya yi wannan roƙo ne a ranar Alhamis lokacin da shugabancin majalisar ya umarci su kada ƙuri’a kan shawarar da Kwamitin Ladabtarwa da Hakkokin Majalisa ya gabatar na dakatar da ita.

Kara karanta wannan

Zargin lalata: Akpabio ya tono abin da ya faru a daren auren Sanata Natasha

Natasha
Majakisa ta ki amince wa da rage watanni dakatar da Natasha Hoto: Godswill Obot Akpabio/Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

A cikin wani bidiyo da Arise News ta wallafa a shafin X, Moro ya amince cewa Sanatar ta Kogi ta saba wa dokokin majalisa dangane da sauya wurin zama a zauren majalisa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A sassauta wa Natasha," Sanata Moro

Sanata Moro, wanda ya kwatanta Natasha Akpoti-Uduaghan da ɗa mai taurin kai, ya roƙi majalisa da ta rage wa’adin dakatarwarta daga watanni shida zuwa watanni uku.

Roƙon da ya yi na zuwa ne bayan da kwamitin ladabtarwa ya bayar da shawarar dakatar da Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida.

Natasha
Majalisa ta dakatar da Natasha Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Da yake jawabi, Sanata Abba Moro ya ce:

"Ba mu adawa da rahoton kwamitin. Amma, Mai girma Shugaban Majalisa, ina so in tunatar da kowa cewa mu ‘yan Najeriya ne, kuma muna da wata al’ada da ke cewa idan ka doke yaro da hannun dama, sai ka jawo shi da hannun hagu.
"Saboda haka, majalisar dattawa na sane da cewa a gidajenmu ma muna da yaran da ke da taurin kai, amma ba ma korarsu daga gidajenmu! Sai dai mu ci gaba da jan hankalinsu don su gyara halayensu."

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Majalisar dattawa ta dakatar da sanatar Kogi na tsawon watanni 6

Majalisar dattawa ta dakatar da Natasha

Duk da roƙon da Moro ya yi, shugabancin majalisar dattawa ya amince da shawarar kwamitin ladabtarwa na dakatar da Akpoti-Uduaghan na watanni shida.

A cikin hukuncin, an yanke cewa za a dakatar da albashinta, za a cire jami’an tsaron da ke tare da ita.

Abin bai tsaya nan ba, daga cikin ukubar shi ne za a hana ta shiga harabar majalisar dokoki sannan kuma za a rufe ofishinta.

Haka kuma masu taimaka mata a harkokin majalisa ba za su sami albashinsu ba a lokacin dakatarwar.

Natasha ta nanata zarginta a kan Akpabio

A baya, mun wallafa cewa Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta sake miƙa ƙorafi kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, bisa zargin cin zarafi.

Natasha, wacce ita ce shugabar kwamitin majalisar dattawa kan mazauna ƙasashen waje da ƙungiyoyi masu zaman kansu, ta gabatar da sabon ƙorafin ne bayan an yi watsi da na farko.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng