Ta Faru Ta Kare: Majalisar Dattawa Ta Dakatar da Sanatar Kogi na Tsawon Watanni 6

Ta Faru Ta Kare: Majalisar Dattawa Ta Dakatar da Sanatar Kogi na Tsawon Watanni 6

  • Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bisa shawarar kwamitin ladabtarwa karkashin Sanata Neda Imasuen
  • Rahoto ya nuna cewa Natasha za ta fuskanci dakatarwa na watanni shida daga ranar 6 ga Maris, 2025, bisa karya dokokin Majalisar
  • Majalisar ta amince da hana Sanata Natasha ta albashi da alawus, rufe ofishinta, janye jami’an tsaro, da hana ta zuwa ko kusa da majalisar
  • Duk da wannan hukunci, sanatar ta Kogi ta Tsakiya ta ce rashin adalci ba zai taba dorewa ba, tana mai cewa za ta ci gaba da kare kanta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke wakiltar Kogi ta Tsakiya.

Majalisar ta dakatar da Sanata Natasha ne bisa shawarwarin kwamitin da'a da ladabtarwa na majalisar karkashin jagorancin Sanata Neda Imasuen.

Kara karanta wannan

Yadda majalisar dattawa ta yi biris da rokon Sanata kan dakatar da Natasha

Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Natasha kan wulakanta dokokin majalisar
Majalisar dattawa ta sanar da dakatar da Sanata Natasha na tsawon watanni 6. Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Natasha

Rahoton NTA News ya nuna cewa majalisar dattawan ta dakatar da 'yar majalisar na tsawon watanni shida, wanda zai fara daga ranar 6 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoton kwamitin ladabtarwar, Sanata Natasha ta karya wasu dokokin majalisar biyo bayan kalaman da ta yi a kan shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio.

Kwamitin ya gudanar da bincike kan 'yar majalisar ne bayan ta nunawa Akpabio yatsa a zauren majalisar saboda ya canza mata wurin zama.

Matsalar da Natasha za ta shiga bayan dakatarwar

A zaman majalisar dattawan na ranar Alhamis, 6 ga watan Maris, majalisar ta dauki matakin cewa za a garkame ofishin Natasha na tsawon watanni shida.

Majalisar dattawan ta kuma amincewa cewa za a dakatar da albashi da dukkanin alawus alawus din da ake baiwa Sanata Natasha na watannin.

A cikin watannin nan shida da take zaman dakatarwar, majalisar dattawa ta ba da umarnin janye dukkanin wasu jami'an tsaro da ke gadin 'yar majalisar, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Zargin lalata: Akpabio ya tono abin da ya faru a daren auren Sanata Natasha

Hakazalika, majalisar ta ba da umarnin hana Sanata Natasha gabatar da kanta a matsayin wakiliyar majalisar dattawa a cikin gida Najeriya ko wajen kasar nan.

Natasha ta ki nuna nadama bayan wannan hukunci

Majalisar dattawa ta dakatar da albashin sanata Natasha bayan rahoton kwamiti
Shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Natasha. Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Babu Sanata Natasha babu majalisa

Hukuncin majalisar bai tsaya a nan ba, an umarci Sanata Natasha da ta tabbatar ba a kara ganin keyarta a kusa da ginin majalisar dattawan ba.

Baya ga dakatar da ita, kwamitin ya ba da shawarwar cewa Sanata Natasha za ta rubutawa majalisar takardar neman afuwa kan karya dokokin majalisar.

Wannan mataki na majalisar ya sake ruruta rikicin da ke ci gaba da faruwa tsakanin Natasha da shugaban majalisar dattawan, Sanata Godswill Akpabio.

Sai dai kuma, 'yar majalisar dattawan ta ki nuna nadama kan wannan hukunci, ta dage cewa rashin adalci ba zai taba dorewa ba.

'Yan mazabar Natasha sun juya mata baya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugabanni da masu ruwa da tsaki a mazaɓar Kogi ta Tsakiya sun aika wasiƙa ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ƙara shiga tsaka mai wuya, Majalisar Dokoki ta dawo da shirin tsige shi

A cikin wasiƙar, sun nisanta kansu daga halayen wakiliyar tasu, Sanata Natasha Akpoti, tare da bayyana irin gudummawar da Akpabio ya ba ta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng