Tinubu Ya ba da Umarnin Daukan Matasa Aiki a Dukkan Jihohin Najeriya
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa matasa 774 da aka horar a fannin lafiya aiki kai tsaye bayan kammala aikin wucin gadi
- Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da shirin a Abuja, yana mai cewa matasan za su ci gaba da aiki bayan wa’adin shekara guda
- Ministan lafiya, Ali Pate, ya bukaci hukumomin tarayya, jihohi da kananan hukumomi da su yi aiki da matasan a bunkasa kiwon lafiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar da shirin horar da matasa 774 don sa ido kan cibiyoyin kiwon lafiya a fadin Najeriya.
Shugaban ya tabbatar da cewa bayan wa’adin shekara guda, matasan za su samu aiki kai tsaye domin ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Kara karanta wannan
Ramadan: An fadi dalilin faduwar farashin abinci karon farko cikin shekaru 10 a azumi

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da Bola Tinubu ya yi ne a cikin wani sako da hadimin shugaban kasa, Sunday Dare ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton Channels TV ya nuna cewa shirin yana daga cikin manufofin gwamnatin Tinubu na farfado da cibiyoyin kiwon lafiya.
Bola Tinubu ya yarda a dauki matasa aiki
Ma'aikatar lafiya ta bayyana cewa an zabo matasa 774 ne ta hanyar tantancewar cancanta daga cikin masu neman gurbin shiga sama da 359,000.
Matasan da aka zakulo za su yi aiki ne domin lura da cibiyoyin lafiya na shekara daya, amma kuma shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin a dauke su aiki da zarar sun kammala.
Shugaban kasar ya ce:
“ Ina mai tabbatar muku da cewa za ku samu aikin din-din-din. Daga yau, tamkar kun zama ma’aikata ne, za a ci gaba da aiki da ku bayan wa’adin shekara guda.”
Shirin yana da nufin inganta kiwon lafiyar al’umma ta hanyar amfani da sababbin dabaru da kirkire-kirkire a fannin lafiya.
Ana sa ran matasan za su gudanar da aiki a cibiyoyin kiwon lafiya na kananan hukumomi 774 a fadin kasar nan.
Ministan lafiya ya bukaci aiki da matasan
Ministan lafiya, Ali Pate, ya jaddada cewa matasan da aka horar sun cancanci ci gaba da aiki a fannoni daban-daban na kiwon lafiya a Najeriya.
Farfesa Pate ya bukaci hukumomin tarayya, jihohi da kananan hukumomi da su rungume su domin bunkasa kiwon lafiya a Najeriya.
Ministan ya ce shirin zai taimaka wajen cimma burin inganta kiwon lafiya a Najeriya, saboda haka suke bukatar hadin gwiwa domin ci gaba da tafiyar da shi.

Asali: Twitter
Alakar shirin da gwamnatin Tinubu
Shirin na daga cikin manufofin gwamnatin Tinubu na farfado da kiwon lafiya a matakin farko a fadin Najeriya.
Matasan da aka dauka aiki za su kasance masu sa ido da bayar da rahoto kan halin da cibiyoyin kiwon lafiya ke ciki.
Haka zalika, ana sa ran matasan za su taka muhimmiyar rawa wajen inganta kiwon lafiya a yankunansu, wanda zai taimaka wajen rage yawan mace-mace.
Shugaba Tinubu ya yi jinjina ga Obasanjo
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya taya tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 88.
Shugaban kasa Tinubu ya bayyana yadda Obasanjo ya taka rawa sosai wajen hadin kan Najeriya musamman a lokacin yakin basasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng