Zargin Lalata: Majalisa Ta Bayyana Hukuncin da Ya Kamata a Yanke Wa Sanata Natasha
- Kwamitin ladabtarwa na Majalisar Dattawa ya ba da shawarin dakatar da sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti na tsawon watanni shida
- A zaman Majalisa na ranar Alhamis, kwamitin ya bukaci Majalisa ta dakatar da albashinta da duk wani alawus, sannan a janye jami'an tsaronta
- Wannan dai na zuwa ne bayan Natasha ta sake gabatar da ƙorafi kan zargin da take wa shugaban majalisar dattawa watau Godswill Akpabio
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa'a na Majalisar Dattawa ya bada shawarar dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida.
Wannan na zuwa ne bayan da ta yi zargin cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ci zarafinta ta hanyar neman lalata da ita.

Asali: Twitter
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa kwamitin ya ba da shawarar dakatar da ita ne bayan ta ƙi halartar zaman da aka gayyace ta ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamiti ya nemi a dakatar da Sanata Natasha
Bayanin da kwamitin ya fitar ya nuna cewa Sanata Natasha ta saba dokokin majalisa, kuma dole ne ta nemi afuwa saboda abin da aka bayyana da "raini da rashin girmamawa ga majalisa."
Har ila yau, a tsawon lokacin da za ta ɗauka bayan an dakatar da ita, kwamitin ya bada shawarar a dakatar da albashinta da kuma janye duk wani tsaro da aka tanadar mata.
Natasha ta sake miƙa korafi ga Majalisa
Tun farko, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta sake gabatar da takardar korafi kan zargin cin zarfi da take yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, a yayin zaman majalisa.
A wannan karon, ta gabatar da takardar ne a madadin mazabarta bisa jagorancin wani dan yankinta mai suna Zubairu Yakubu.
Bayan tabbatar da cewa babu wata matsala ta shari’a da zai hana gabatar da takardar, Akpabio ya ba ta izinin ajiye ta a gaban majalisar da misalin karfe 12:38 na rana.

Kara karanta wannan
Zargin lalata: Sanata Natasha ta sake yamutsa Hazo, ta yi magana kan dakatar da ita
An mika takardar zuwa ga Kwamitin Ladabtarwa, Da’ar Ma’aikata da Korafe-korafe na Majalisa, wanda Sanata Neda Imasuen daga Edo ta Kudu ke jagoranta.
Daga nan kuma Majalisar ta ba kwamitin kwanaki 14 ya dawo mata da rahoto kan ƙorafin da sanatar ta shigar.
Wannan mataki ya biyo bayan irin wannan korafi da Akpoti-Uduaghan ta gabatar a jiya Laraba, wanda ya haddasa ce-ce-ku-ce a majalisa.
Taƙaddamar Natasha-Akpabio ta kai kotu
Babban mai ladabtarwa, Sanata Mohammed Monguno daga Borno ta Arewa ya yi nuni da dokar Majalisa ta 40, yana mai cewa lamarin na da alaka da wata shari’a da ke tsakanin Natasha da matar Akpabio.
Bayan haka ne kwamitin ladabtarwar ya miƙa shawarwarinsa na farko, inda ya nemi a dakatar da Sanata Natasha na tsawon watanni 6, ruwayar Punch.
Akpabio ya tuna lokacin auren Natasha
A wani rahoton, kun ji cewa Godswill Akpabio ya bayyana cewa a masana'antar simintin Dangote da ke Obajana, ya kwana a ranar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi aure.
Shugaban Majalisar Dattawan ya faɗi haka ne domin nuna kusancinsa da Sanata Natasha da mijinta, a yayin da take zarginsa da ci mata zarafi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng