Faɗa Ya Kaure da Mutanen Gari kan Ruwan Sha a Watan Azumi, An Yi Kisa

Faɗa Ya Kaure da Mutanen Gari kan Ruwan Sha a Watan Azumi, An Yi Kisa

  • Mutum ɗaya ya rasa ransa a wata taƙaddama tsakanin mutanen gari da makiyaya kan ruwan sha a wani kauyen Abuja
  • Bayanai sun nuna makiyayan ne suka fara tsokano fitina da suka tura shanunsu cikin wani tafkin da ake amfani da shi
  • Lamarin ya haddasa cacar baki tsakanin mutanen kauyen Riwaza da makiyaya, har ta kai ga mutum ɗaya ya rasa ransa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ana zargin wasu makiyaya da kashe wani mutum mai suna John Moses Gwatana a kauyen Riwaza, yankin Kwali a Abuja.

An tattaro cewa mutumin ya rasa ransa ne yayin da faɗa ya shiga tsakaninsa da wasu makiyaya kan tafkin ruwan da ke yankin.

Taswirar Abuja.
Mutum 1 ya mutu da faɗa ya kaure tsakanin makiyaya da mutanen gari kan ruwan sha Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wani mazaunin kauyen, Yakubu Gideon, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 11:23 na safe, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Kara karanta wannan

Farashin man fetur ya kama hanyar ƙara araha, sauƙi zai lulluɓe ƴan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asalin dalilin ɓarkewar fada da mutanen gari

Ya ce wasu makiyaya sun kawo shanunsu zuwa tafkin domin su sha ruwa, lamarin da ya sa suka gurɓata ruwan da mutanen kauyen ke amfani da shi.

Yakubu Gideon ya bayyana cewa rikicin ya fara ne lokacin da wasu mata suka je tafkin domin diban ruwa, sai suka tarar da shanu suna shan ruwa a wurin.

Hakan ya fusata su, har suka fara taƙaddama da musayar yawu da makiyayan kan yadda suka ɓata masu ruwan da mutane ke sha da girki da shi.

A cewarsa, yayin da takaddamar ke ƙara kamari, wasu daga cikin matan sun koma kauyen domin sanar da mutane abin da ke faruwa.

Ya ce da suka ji haka, marigayin watau mutumin da aka kashe tare da wasu mutane biyu suka garzaya tafkin domin tattaunawa da makiyayan.

Yakubu ya ce da suka isa wurin, sai suka tambayi makiyayan dalilin da yasa suka bari shanunsu suka gurɓata tafkin da ke zama tushen ruwa ga daukacin mutanen kauyen.

Kara karanta wannan

Sanatoci 18 sun gamu da matsala, an hana jirgin saman da ya ɗauko su sauka

Makiyaya sun kashe mutum 1

"A lokacin, rikicin ya dauki wani sabon salo, inda daya daga cikin makiyayan ya zaro adda ya sare daya daga cikin mazauna garin," in ji shi.

Bisa bayanin Yakubu Gideon, mutane biyu sun samu raunuka, yayin da wanda ya fi samun munanan raunuka ya rasu a hanyar kai shi asibiti a kauyen Fogbe da ke makwabtaka da su.

Mutanen biyu da suka ji raunuka an garzaya da su wani asibiti da ke Gwagwalada domin samun kulawa.

Kofar shiga Abuja.
An kashe mutum 1 a rigimar da ta faru kan ruwan sha a Abuja Hoto: Abuja
Asali: Getty Images

Ƴan banga sun kai ɗauƙi

Makiyayan dai sun tsere da shanunsu kafin zuwan ‘yan banga daga kauyen Fogbe. Daga baya, an gano cewa makiyayan sun fito ne daga kauyen Zago da ke jihar Neja.

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin amma ta umarci manema labarai da su tuntubi hedikwatar ‘yan sanda ta Abuja domin karin bayani.

Sai dai, har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ba ta fitar da sanarwa a hukunance kan lamarin ba.

Kara karanta wannan

Boko Haram ta tsallaka, ta kai harin ramuwar gayya a Neja, ta kashe bayin Allah

An kama tsohon jami'in NIS da makami

A wani labarin, kun ji cewa dakarun ƴan sanda sun cafke tsohon jami'in hukumar NIS bisa zarginsa da sayarwa ƴan bindiga makamai.

Tsohon jami'in wanda ba a bayyana sunansa ba an kama shi ne bayan wani aikin bincike da ƴan sanda suka gudanar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262