‘Yadda Na Yi Watsi da Sunan da Iyayena Suka Rada Mani’: Obasanjo Ya Yi Fallasa

‘Yadda Na Yi Watsi da Sunan da Iyayena Suka Rada Mani’: Obasanjo Ya Yi Fallasa

  • Olusegun Obasanjo ya ce ya daina amfani da sunan Matthew da iyayensa suka sanya saboda ba ya son shi ko kadan a rayuwarsa
  • Cif Obasanjo ya bukaci 'yan Afrika su rabu da sunayen da suka samo asali daga mulkin mallaka da cinikin bayi a zamanin baya
  • Tsohon shugaban kasar ya ce har yanzu Afrika na fama da tasirin mulkin mallaka da ya hana ci gaba ta bangarori da dama
  • Ya bayyana cewa yana da cikakken fata cewa Najeriya za ta zama kasa mai girma da kuma samun ci gaba a bangarori da dama

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya shawarci yan Afirka kan rike al'adunsu fiye da biyewa na Turawa da ke yi musu illa.

Obasanjo ya bayyana cewa ya daina amfani da sunan Matthew da iyayensa suka laka masa saboda ba ya son shi ko kadan.

Kara karanta wannan

Obasanjo @ 88: Tinubu ya jinjina, ya jero alheran tsohon shugaban Najeriya

Obasanjo ya fadi sunan da iyayensa suka laka masa wanda bai so
Olusegun Obasanjo ya shawarci yan Afirka kan amfani da sunan Turawa. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Obasanjo ya magantu kan wutar Mambilla

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin wani taron gabatar da littafi da aka shirya don murnar cika shekaru 88 da haihuwarsa a Abeokuta, Jihar Ogun, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A baya, Legit Hausa ta ruwaito cewa Olusegun Obasanjo ya ce ba wanda ya tura shi bayar da shaida kan rikicin kwangilar Mambilla a Paris.

Obasanjo ya ce ya yanke shawarar bayar da shaida ne domin gyara wasu bayanai da tsohon ministan wuta, Olu Agunloye, ya fada.

Hakan ya biyo bayan neman diyyar $2.3bn daga Najeriya da kamfanin Sunrise Power ya yi bayan ya zargi kasar da karya yarjejeniyar aikin tashar wutar.

Obasanjo: "'Yan Afirka su rike al'adunsu"

A yayin jawabinsa, Obasanjo ya bukaci 'yan Afrika su daina amfani da sunayen da suka samo asali daga mulkin mallaka da cinikin bayi.

Ya ce har sai Afrika ta samu 'yanci daga wadannan tasirin, ba za ta iya cimma ci gaba na hakika ba.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito da aka yada labarin Allah ya karbi rayuwar fitaccen basarake

Obasanjo ya bayyana cewa har yanzu Afrika na fama da tasirin cinikin bayi da mulkin mallaka ta wasu hanyoyi.

Obasanjo ya shawarci yan Afrika kan amfani da sunan Turawa
Cif Olusegun Obasanjo ya nuna damuwa kan yadda yan Afirka ke amfani da sunan Turawa. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Obasanjo ya yi wa yan Najeriya albishir

Ya ce idan ana so a samu ci gaba, dole ne a kawar da tasirin wadannan abubuwa daga rayuwar al’umma.

Dangane da makomar Najeriya, Obasanjo ya ce yana da cikakken fata cewa kasar za ta samu ci gaba sosai a rayuwarsa.

Ya ce duk da halin da ake ciki, yana da tabbacin Najeriya za ta zama kasa mai girma da kowa zai yi alfahari da ita.

Tinubu ya taya Obasanjo murnar ranar haihuwa

Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yabawa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, a yayin cikarsa shekaru 88 a duniya.

Tinubu ya bayyana Obasanjo a matsayin gwarzo da ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Najeriya da kuma dunkulewar kasa musamman a lokacin mulkinsa daga 1999 zuwa 2003.

Kara karanta wannan

Bauchi: Miji ya yi wa matarsa dukan tsiya har ta zarce lahira kan abincin Ramadan

Shugaban ya roƙi Allah ya ƙara wa Obasanjo lafiya da tsawon rai domin Najeriya da Afirka su ci gaba da amfana da hikimominsa duba da irin kwarewarsa a bangarori da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng