Makusancin Kwankwaso, Buba Galadima Ya Hango Illar Saukar Farashin Abinci

Makusancin Kwankwaso, Buba Galadima Ya Hango Illar Saukar Farashin Abinci

  • Fitaccen dan siyasa, Injiniya Buba Galadima, ya ce saukar farashin abinci da ake gani a halin yanzu na iya haifar da matsaloli a nan gaba
  • A cewarsa, shigo da kayan abinci daga kasashen waje zai kassara manoman Najeriya tare da durkusar da masana’antun sarrafa abinci
  • Buba ya yi gargadin cewa shigo da kayan abinci daga ketare zai sa Najeriya ta gaza ciyar da kanta, wanda zai haifar da matsala a nan gaba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Fitaccen 'dan siyasa a Najeriya, Injiniya Buba Galadima, ya ce faduwar farashin kayan abinci da ake gani a halin yanzu ba abin farin ciki ba ne.

Buba Galadima, wanda makusancin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne, ya ce akwai yiwuwar sakamakon saukar farashin kayan abinci ya haifar da matsaloli masu girma a nan gaba.

Kara karanta wannan

Yadda Biden da Amurka su ka matsawa Najeriya lamba, aka saki jami'in Binance

Galadima
Buba Galadima ya soki tsarin shigo da abinci Najeriya Hoto: Bola Tinubu/Getty images
Asali: Getty Images

A wata hira da ya yi da DCL Hausa, dattijon dan siyasar ya ce matakan da gwamnatin Bola Tinubu ta dauka na karya farashin abinci ba za su haifar da abin da mai ido zai ji daɗi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa, maimakon shigo da kayan abinci daga ketare, kamata ya yi gwamnati ta karfafa wa manoman cikin gida gwiwa ta hanyar samar musu da kayan noma na zamani.

Buba Galadima ya soki tsarin gwamnatin Tinubu

Buba Galadima ya kara da cewa masana’antun shinkafa da sauran masana’antun sarrafa abinci a Najeriya za su fuskanci babbar matsala saboda shigo da abinci daga ketare.

Tinubu
Buba Galadima na ganin tsarin Tinubu zai jawo matsala Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya shaida cewa kamfanonin za su fada cikin mawuyacin hali, domin shigo da abinci zai hana su mayar da jarin tiriliyoyin Naira da ‘yan kasuwa suka zuba wajen kafa masana’antunsu.

Dalilin Buba Galadima na sukar matakin gwamnati

Fitaccen dan siyasar ya ce babu alfanu a rage farashin kayan abinci ta hanyar shigo da masara da shinkafa daga kasashen ketare.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya

A cewarsa, matakin zai kashe kasuwar manoman gida, domin jama’a za su fi dogara da abinci daga waje, maimakon wanda ake nomawa a Najeriya.

Ya ce:

"An kassara manoma, ba za su iya zuwa gona su yi noma ba, domin noman da za su yi bai kai na kasashen waje ba wajen arha da sauki."

Buba ya zargi gwamnati da shigo da abinci

Injiniya Buba Galadima ya zargi gwamnatin tarayya da shigo da abinci kai tsaye, duk da cewa manoman Najeriya ba su samu damar yin noman da zai rage farashin kaya ba.

Ya bayyana damuwa kan shigo da abinci daga kasashen waje, yana mai cewa hakan zai jefa Najeriya cikin dogon hali na dogaro da abinci daga ketare.

Ya ce:

"Abu na farko shi ne, gwamnati ta zage damtse, ta koya wa manoma yadda ake noma irin na zamani. Ta kawo na’urori na zamani yadda noman zai samu sauki, sannan abinci ya yi sauki don dole."

Kara karanta wannan

Dalibai sun fusata kan rufe makarantu a Arewa, NANS ta shirya zanga-zanga

A cewarsa, noman gargajiya da ake yi ba zai haifar da sakamakon da ake bukata ba, ganin cewa akwai bakin da ke bukatar a ciyar da su da yawa a Najeriya.

Tinubu ya magantu kan farashin abinci

A baya, mun wallafa cewa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya danganta saukar farashin kayan abinci a Najeriya da irin manufofin da gwamnatinsa ta bijiro da su don samar da sauki.

Shugaban, wanda ya fadi haka a taron kwamitin zartarwa na APC da ya gudana a Abuja, ya dauki alkawari cewa gwamnati za ta zage damtse domin samar da sauki mai dorewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng