"Tsautsayi Ya Gitta": Sama da Mutum 20 Sun Mutu a Wani Yanayi a Watan Ramadan

"Tsautsayi Ya Gitta": Sama da Mutum 20 Sun Mutu a Wani Yanayi a Watan Ramadan

  • Yayin da musulmai suka shiga watan azumin Ramadan, wasu mutane 20 sun rasa rayukansu sakamakom haɗurran motoci a jihohi uku
  • An ruwaito cewa mutum 16 sun mutu a jihar Ogun, biyu a Oyo da kuma mutum huɗu a jihar Kogi duk a sanadiyyar hatsarin motoci
  • Hukumar kiyaye haɗurra watau FRSC ta shawarci direbobi su daina gudun wuce ƙima kuma su riƙa bin dokokin tuƙi da na hanya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun - Akalla mutum 20 ne suka rasa rayukansu a hadduran mota daban-daban da suka faru a jihohin Ogun, Kogi da Oyo a daidai lokacin da azumin Ramadan ya kankama.

A jihar Ogun, mutum 16 sun kone kurmus a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a motar Mazda, yayin da wasu uku suka jikkata.

Kara karanta wannan

Yadda sufetan 'dan sanda da matasa suka lakadawa tsinannen duka ya rasu a Jos

Jami'an FRSC.
Sama da mutum 20 sun raa rayukansu a jihohi 3 a watan Ramadan Hoto: FRSC
Asali: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa a Kogi, mutum hudu sun mutu a wani hatsari da ya shafi babbar mota, sai kuma mutum biyu da suka kone a wani gidan mai a Oyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutum 16 sun ƙone a Ogun

A jihar Ogun, hatsarin ya faru ne a yankin Buhari Estate da ke kan titin Abeokuta-Sagamu, ranar Talata.

Wata farar motar Mazda mai lamba KJA 949 YJ ce ta kama da wuta, ta lakume rayukan mutum 16.

Mai magana da yawun Hukumar Kiyaye Hadurra ta Ƙasa (FRSC), Florence Okpe, ta ce ba a iya tantance jinsi ko asalin gawawwakin ba saboda sun kone gaba ɗaya.

Ta bayyana cewa motar tana ɗauke da bututun gas wanda ya fashe kuma wuta ta kama suna cikin tafiya.

"An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Tarayya na Idi Aba a Abeokuta, su kuma gawawwakin ba mu kai ga ɗauke su ba yanzu," in ji ta.

Kara karanta wannan

Boko Haram ta tsallaka, ta kai harin ramuwar gayya a Neja, ta kashe bayin Allah

Hadari ya jawo mutum 4 sun mutu a Kogi

A jihar Kogi, mutum hudu sun mutu a hatsarin da ya faru da wata babbar mota a yankin Falele, kan hanyar Lokoja-Okene, ranar Litinin da misalin ƙarfe 7:20 na dare.

Kwamandan FRSC na jihar, Samuel Oyedeji, ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudu da kuma lalacewar birki, wanda ya sa motar ta bugi tubalin raba titi.

Ya ce tuni aka kai waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Honey Gold don samun kulawa, yayin da aka ajiye gawawwakin a asibitin koyarwa na tarayya a Lokoja.

Gobara ta yi ajalin mutum 2 a jihar Oyo

A jihar Oyo kuma, mutum biyu sun mutu bayan da wata motar dakon mai ta kama da wuta a gidan man Gabstab Mega Petrol Station da ke Orita Challenge, Ibadan.

Babban Manajan hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, Yemi Akinyinka, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa hatsarin ya faru ne sakamakon lalacewar birki.

Kara karanta wannan

"Ku bi a hankali," Omokri ya bukaci CAN ta guji shari’a da jihohi kan hutun Ramadan

Taswirar Oyo.
An rasa rayuka sanadiyyar tashin gobara a gidan mai a Oyo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ya ce hakan ya sa tankar ta zubar da man fetur sannan ta kama da wuta. Direban tankar da yaronsa sun kone ƙurmus.

Hukumar FRSC ta shawarci direbobi da su guji gudun wuce kima da kula da lafiyar motocinsu don kaucewa irin waɗannan haɗurran.

Daliban Jami'a 5 sun mutu a hatsari

A baya, kun ji cewa wata babba motar dakon kaya ta murkushe ɗalibai biyar har lahira a yankin Felele da ke jihar Kogi.

Jami’ar Tarayya da ke Lokoja (FUL) a jihar Kogi ta shiga jimami bayan mummunan hadarin motar ya yi sanadin mutuwar dalibanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng