Ana Fargaba a Kano Bayan Hukuncin Kotun Koli kan Zaben Kananan Hukumomi a Ribas
- An shiga fargaba bayan babbar kotun tarayya ta yanke hukunci a kan dambarwar zaben kananan hukumomin jihar Ribas
- Ana zaman jiran yadda za ta kaya a karar da APC ta shigar a gaban kotu ta na kalubalantar zaben kananan hukumomin Kano
- Babbar kotun tarayyar ta soke zabukan kananan hukumomin Ribas, ta bayyana cewa an take dokokin kasa yayin shirya zaben
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Hukuncin da Kotun Koli ta yanke kwanan nan na soke zaben kananan hukumomi a Jihar Ribas na kara haddasa fargaba a Kano.
An shiga fargaba kan yadda alkalin babbar kotun tarayya, Mai shari’a Simon Amobeda, zai yanke hukunci kan shari'ar da ke gabansa a kan zaben kananan hukumomin jihar.

Source: Facebook
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa a karar da jam’iyyar APC mai mulki ta shigar, Kotun Koli, ta yanke hukunci da cewa zaben kananan hukumomi a Jihar Ribas bai inganta ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamitin alkalai biyar na kotun da ya yanke wannan hukunci ya tabbatar da cewa an yi zaben ba tare da bin ka’idojin doka ba.
Jam'iyyar APC ta kai gwamnatin Kano kotu
Jam’iyyar APC tare da wasu masu ruwa da tsaki sun maka gwamnatin Kano, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar (KANSIEC), da wasu mutane 55 a gaban kotu.
Daga cikin wadanda aka kai gaban kotu har da shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar bisa zargin gudanar da zaben kananan hukumomi ba bisa ka'ida ba.
APC na bukatar kotu ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN), Kwamitin Raba Kudin Gwamnati da wasu hukumomin gwamnati da su dakatar da rabon kananan hukumomin Kano.
Masu karar na neman kotu ta ayyana cewa shugabannin kananan hukumomi 44 na Kano ba a zabe su ta hanyar dimokuradiyya ba, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun yi bayanin yadda bindigogi kusan 4,000 suka bace a karkashin kulawarta
Halin da shari'ar APC-Kano ke ciki a yau
A zaman kotu na karshe, rashin halartar babban lauya Cif Adegboyega Awomolo (SAN), wanda ke kare gwamnatin Kano, ya jawo tsaikon ci gaba da sauraron shari’ar.
Mai shari’a Amobeda ya bayyana wa kotu cewa Awomolo ya aika da takardar neman a dage shari'ar har bayan hutun bukukuwan Easter.

Source: Facebook
Sai dai alkalin ya yi watsi da bukatar da Awomolo ya gabatar, yana mai cewa karar ta dade tana fuskantar kalubale, lamarin da ke yin illa ga shari'ar da ake yi.
Duk da haka, Mai shari’a Amobeda ya dage shari’ar zuwa 14 ga Afrilu, 2025, amma ya bayar da umarni sada bangarorin da ke cikin shari'ar da takardun kotu a kan batun.
Kano: Fashin bakin masana kan hukuncin Ribas
A wata tattaunawa da Legit, wani lauya a Kano, Barista Ibrahim Kiyawa ya bayyana cewa an yanke hukunci kan zaben kananan hukumomi a Ribas bisa kwakkwaran dalilai na shari’a.
Ya ce:
"A kan maganar Kano, wannan batu na gaban kotu ne. Tun da kotu ba ta yanke hukunci ba, ba za a iya cewa an yi daidai ko ba a yi daidai ba."
Ya kara da cewa shari’ar na da matukar sarkakiya, domin dokokin kasa ba su yarda a rika bayyana ra’ayi kan hukuncin da ake jira kotu ta yanke ba.
An kaddamar da ciyar wa a jihar Kano
A baya, mun wallafa cewa Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam, ya jagoranci kaddamar da shirin ciyar da masu azumi a lokacin bude baki na shekarar 2025.
Wannan shiri dai wani yunkuri ne na gwamnatin Abba Kabir Yusuf na tallafa wa al’ummar da ke bukatar taimako a wannan wata mai alfarma, inda mutane akalla 91,000 za su amfana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

