'Yan Ta'adda Sun Dura Gidan Jami'in Ɗan Sanda a Yobe, Sun Yiwa Ƴaƴansa Yankan Rago

'Yan Ta'adda Sun Dura Gidan Jami'in Ɗan Sanda a Yobe, Sun Yiwa Ƴaƴansa Yankan Rago

  • Wasu 'yan ta'adda da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari gidan jami’in ‘yan sanda a Buni Yadi, jihar Yobe, suka kashe ‘ya’yansa biyu
  • Jami’in tsaron ya samu damar tsere ta katanga, amma ‘yan ta’addan sun kashe ‘ya’yansa masu shekaru 25 da 27 tare da kone gawarwakinsu
  • Bayan faruwar wannan lamari, mazauna yankin Buni Yadi sun sake shiga fargaba kan yawaitar hare-haren 'yan ta'adda da ake samu a yankin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Yobe - Wasu 'yan ta'adda da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun afka gidan wani jami’in ‘yan sanda, Malam Jibrin, suka kashe ‘ya’yansa biyu a garin Buni Yadi.

Bayan sun kashe matasan guda biyu, sun kuma banka wa gawarwakinsu wuta tare da kone gidan gaba ɗaya a yankin da ke Gujba, jihar Yobe.

Kara karanta wannan

'Dan bindiga ya tono sirrin 'yan ta'adda ga sojoji kafin 'yan uwasa su harbe shi

'Yan ta'adda sun kai hari gidan wani dan sanda a Yobe, sun kashe 'ya'yansa
'Yan ta'adda sun kashe 'ya'yan wani dan sanda a Yobe a wani hari da suka kai gidansa. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

'Yan ta'adda sun kashe 'ya'yan dan sanda

Rahotan jaridar Daily Trust ya nuna cewa harin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na safiyar ranar Litinin a unguwar Shuwari Babban Layi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa Malam Jibrin, wanda shi ne jami’in bincike a ofishin ‘yan sanda na Buni Yadi, yana cikin gida lokacin da aka kai harin.

Majiyar ta ce:

"Dan sanda ya yi nasarar tsallake katanga ya tsere. Hakan ya fusata ‘yan ta’addan, inda suka yiwa ‘ya’yansa masu shekaru 25 da 27 yankan rago.
"Bayan kashe matasan, ‘yan ta'addan sun kuma kona gawarwakinsu da gidan gaba ɗaya, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargici."

'Dan sa-kai ya fadi maboyar 'yan ta'adda a Yobe

Wani ‘dan sa-kai daya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa jaridar cewa maharan suna zaune ne a yankin Buk da Talala, kimanin kilomita 30 daga Buni Yadi.

"A halin yanzu, ba wanda ke iya shiga yankin Damboa. Hatta su kansu sojoji sun san da irin hatsarin da ke tattare da wannan wuri"

Kara karanta wannan

Karfin hali: 'Yan bindiga sun sace babban jami'in dan sanda a Abuja

- Inji dan sa-kan.

Ya kuma ce a yankin ne ‘yan ta’adda suka kai hari kan sojoji a bara, kuma suka kashe kwamandan soja da wasu sojoji da ‘yan sa-kai.

Wasu mazauna Buni Yadi sun ce hare-haren da ke faruwa kwanan nan sun sa mutane cikin tsananin fargaba da rashin kwanciyar hankali.

Mazauna Buni Yadi sun fadi halin da suke ciki

Mazauna Buni Yadi sun fadi halin da suke ciki game da matsalar tsaro
Mazauna Buni Yadi, jihar Yobe sun shiga tashin hankali da aka kashe 'ya'yan dan sanda. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wani mazaunin yankin, Muhammad Garba, ya bayyana cewa yanzu mutane ba sa iya barci cikin nutsuwa saboda yawaitar hare-haren.

"A yanzu, babu inda ke da aminci. Ko a cikin gari ko a kan hanya. Gaskiya mutane sun shiga tsaka mai wuya," inji Muhammad Garba.

Harin da aka kai ya kara tsananta tsoron da mutane ke ciki, musamman a garin Buni Yadi, wanda ke kusa da garin Gwamna Mai Mala Buni.

Har yanzu hukumomi ba su fitar da wata sanarwa kan harin ba, yayin da al'umma suke ci gaba da kira ga jami'an tsaro su tsananta farautar 'yan ta'addar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mutane 10, sun sace ɗaliban jami'a 4 a wasu jihohin Arewa

An tsinci gawar babban jami'in 'dan sanda a otel

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an gano gawar Sufeta Haruna Mohammed a cikin ɗakin wani otal da ke Ogun, lamarin da ya sa hukumomi suka fara bincike.

An rahoto cewa Sufeta Haruna da ke aiki a ofishin ‘yan sanda na Ishashi, Legas, ya shiga otal ɗin Super G Royal da wata mace da misalin ƙarfe 1:00 na daren Asabar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.