Yobe: An kashe kwamandan rundunar soji da wasu sojoji 20 a sabon harin kwanton bauna

Yobe: An kashe kwamandan rundunar soji da wasu sojoji 20 a sabon harin kwanton bauna

Wani kwamandan rundunar soji da karin wasu dakarun sojoji a kalla 20 sun mutu sakamakon wani harin kwanton bauna da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai musu a jihar Yobe.

Mayakan sun kai wa tawagar sojojin harin kwanton baunar ne a hanyarsu ta zuwa wani sansanin sojoji da ke Benisheikh bayan sun dawo daga Borogozo, inda rundunar soji 29 ke da sansani.

Wata majiyar soji a hedikwatar rundunar soji ta 'Ofireshon Lafiya Dole' ta shaida wa jaridar 'The cable' cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Laraba.

"Su na kan hanyarsu ne ta zuwa Benisheikh lokacin da aka kai mus harin. Sun kashe kwamandan rundunar soji, mai mukamin kanal, da kuma dakarun sojoji a kalla su 20," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Abinda ya sa na yi aure har sau bakwai - Jaruma Sadiya Kabala

An tura wasu karin dakarun soji domin su kai wa rundunar sojojin agaji, amma su ma an kashe kwamandansu, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, Musa Sagir, kakakin rundunar soji na kasa, bai amsa sakon wayar hannu da jaridar The Cable ta aika masa ba domin jin ta bakin rundunar soji a kan harin da aka kai wa sojojin a jihar Yobe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel