'Yan Bindiga Sun Yi Ɓarna a Arewa Maso Yamma, An Kashe Mutane 12,000

'Yan Bindiga Sun Yi Ɓarna a Arewa Maso Yamma, An Kashe Mutane 12,000

  • Rabaran Matthew Hassan Kukah ya ce mutane 12,000 sun mutu a Arewa maso Yamma sakamakon hare-haren ‘yan bindiga
  • Ya bayyana cewa kashi 76% na sace-sacen mutane a Arewacin Najeriya sun fi faruwa a yankin na Arewa maso Yamma
  • Rabaran Kukah ya yi wannan bayani ne a wajen taron Arewa maso Yamma kan mata, zaman lafiya da tsaro, da aka yi a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida Abuja - Shugaban Cocin Katolika da ke jihar Sokoto, Rabaran Matthew Hassan Kukah, ya ce mutane 12,000 sun mutu a Arewa maso Yamma.

Babban malamin addinin Kiristan, ya ce 'yan bindiga, 'yan ta'adda, da sauran kungiyoyin tada ƙayar baya suka kashe mutanen a cikin shekaru 10.

Shugaban Cocin Katolika na Sokoto, Rabaran Kukah ya yi magana kan ta'addanci a Arewa maso Yamma
Rabaran Kukah ya ce aƙalla mutane 12,000 ƴan ta'adda suka kashe a Arewa maso Yamma. Hoto: @FrUgochukwu
Source: Twitter

An gudanar da taron Arewa maso Yamma a Abuja

Matthew Kukah ya bayyana cewa kashi 76% na garkuwa da mutane a Arewacin Najeriya sun fi faruwa a yankin Arewa maso Yamma, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sadu da shugaban MTN, mutum na 1 da ya fi kwasar albashi mai tsoka a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban cibiyar Kukah (TKC) ya yi wannan bayani ne a Abuja, yayin taron Arewa maso Yamma kan mata, zaman lafiya da tsaro, karo na biyu.

An shirya taron ne karkashin jagorancin kungiyar Global Rights Nigeria, tare da hadin gwiwar cibiyar TKC da wasu kungiyoyi masu zaman kansu.

Kungiyoyi irinsu kungiyar tallafawa mabuƙata da jin ra'ayin jama'a ta Isa Wali tare da tallafin UK Aid sun taka rawa wajen shirya wannan taron.

Arewa ta Yamma na fuskantar hare-haren ƴan bindiga

Rabaran Kukah ya ce an samu fiye da hare-hare 4,500, ciki har da garkuwa da mutane da suka faru a Arewa maso Yamma a shekaru 10.

Ya ce fiye da kashi 76% na sace-sacen da ake yi a Arewacin Najeriya suna faruwa ne a wannan yanki na Arewa maso Yamma.

Malamin addinin ya ce yankin ya zama mabuyar masu aikata miyagun laifuffuka, yana mai bukatar hadin kai don shawo kan matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya

Ya jaddada cewa mata suna da rawar da za su taka wajen karfafa zaman lafiya da bunkasa juriyar al'umma kan abubuwan da ke faruwa.

Rabaran Kukah ya yi kira ga jama’a da su hada kai, su manta da bambancin addini da siyasa wajen tunkarar matsalar tsaro da ke addabarsu.

Kungiyoyi sun kawo hanyar magance rikice-rikice

Rabaran Kukah ya yi magana kan rikice-rikice a Arewa maso Yamma.
Rabaran Kukah ya halarci taro kan matsalolin tsaro da suka addabi Arewa maso Yamma. Hoto: @Ekwulu
Source: Twitter

A nata bangaren, Daraktar Global Rights, Abiodun Baiyewu, ta ce matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yamma na kara tsananta cikin shekara 10.

Abiodun ta ce an shirya taron ne domin tattauna matsalar tsaro, da kuma ba da himma wajen samar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.

Ta jaddada cewa zaman lafiya yana bukatar hadin gwiwar shugabannin al’umma, jami’an tsaro, matasa, mata, da kowane dan kasa.

Daraktar Partners West Africa, a Nigeria (PWAN –Nigeria), Kemi Okenyodo, ta ce mata suna da muhimmiyar rawa a kokarin magance rikice-rikicen da ke faruwa.

Ta ce an saka mata a shirin zaman lafiya don daidaito, da kuma zama hanya ta magance rikice-rikice da tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al'umma.

Kara karanta wannan

An tsallake Tinubu, Atiku an ba Kwankwaso lambar karramawa a Najeriya

Taron ya bukaci hadin gwiwar kungiyoyi, shugabanni, da al’umma don magance rashin tsaro da dawo da martabar yankin Arewa maso Yamma.

Tinubu ya nada shugabannin hukumar NWDC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya naɗa sababbin 'yan majalisar gudanarwa na Hukumar Raya Arewa Maso Yamma (NWDC).

Hadimin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya sanar da hakan, yana mai cewa sabbin shugabannin za su taimaka wajen bunƙasa ci gaban yankin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com