An Shiga Tashin Hankali a Bauchi: 'Dan Shekara 20 Ya Kashe Mahaifiyarsa da Tabarya

An Shiga Tashin Hankali a Bauchi: 'Dan Shekara 20 Ya Kashe Mahaifiyarsa da Tabarya

  • Ana zargin wani matashi, Safiyanu Dalhatu ya hallaka mahaifiyarsa da tabarya a Bauchi, lamarin da ya jefa al’umma a firgici da jimami
  • Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kama wanda ake zargi tare da kwace tabaryar da ya yi amfani da ita wajen aikata wannan aika-aika
  • Binciken farko na 'yan sandan ya nuna rikici tsakanin Safiyanu da mahaifiyarsa ne ya harzuka matashin har ya farmaki gyatumarsa
  • Yanzu an dorawa sashen binciken laifuffukan ta'addanci na jihar (SCID) alhakin gudanar da bincike, a gurfanar da wanda ake zargi a kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - An shiga tashin hankali a jihar Bauchi yayin da wani matashi, Safiyanu Dalhatu, ya yi amfani da tabarya ya rika dukan mahaifiyarsa har sai da ta mutu.

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama matashin, dan shekara 20 da ake zargi, a unguwar Abujan Kwata da ke kwaryar jihar.

Kara karanta wannan

An tsallake Tinubu, Atiku an ba Kwankwaso lambar karramawa a Najeriya

Rundunar 'yan sanda ta yi magana da ta kama matashin da ya kashe mahaifiyarsa da ta tabarya
'Yan sanda sun cafke matashin da ake zargin ya kashe mahaifiyarsa da tabarya. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Mai sharhi kan lamuran tsaro a Arewa maso Gabas da kuma yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya fitar da rahoton a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bauchi: Matashi ya kashe mahaifiyarsa da tabarya

A cikin wata sanarwa, kakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya bayyana cewa lamarin ya faru ranar 24 ga Fabrairu da misalin karfe 3:00 na rana.

Rahoton ya nuna cewa kwamitin tsaro da sulhu na Unguwar Abujan Kwata su ne suka kai karar faruwar lamarin ga 'yan sanda.

Kwamitin ya shaidawa 'yan sanda cewa wanda ake zargin ya sanya tabarya mai nauyi ya surfa mahaifiyarsa, lamarin da ya jawo ta kakkarye a hannuwan biyu da ji mata wasu raunukan.

Sanarwar CSP Wakil ta nuna cewa:

"Bayan samun rahoton, DPO na yankin, CSP Abdullahi Muazu, ya debi tawagarsa suka isa wurin da abin ya faru tare da kai matar asibitin ATBUTH domin samun kulawar likita.

Kara karanta wannan

Masu safarar yara sun yiwa 'yan sandan Najeriya tayin cin hancin Naira miliyan 1

"Sai dai abin bakin ciki, likitocin asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, sun tabbatar da mutuwarta."

'Yan sandan Bauchi sun kama matashin

Rundunar 'yan sandan Bauchi ta yi karin haske game da matashin da ake zargin ya kashe mahaifiyarsa
Sashen SCID na rundunar 'yan sandan Bauchi zai binciki matashin da ake zargin ya kashe mahaifiyarsa. Hoto: @BauchiPoliceNG
Asali: Twitter

Binciken farko na ‘yan sanda ya nuna cewa wani sabani da aka samu tsakanin Safiyanu da mahaifiyarsa ne ya jawo yaron ya hau dokin zuciya, ya duke ta da tabaryar.

Kwamishinan ‘yan sanda na Bauchi, CP Auwal Musa Mohammed, ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike don gano gaskiyar dalilin faruwar lamarin.

Sanarwar ta ce an dorawa sashen binciken laifuffukan ta'addanci na ofishin 'yan sandan jihar (SCID) alhakin gudanar da wannan bincike.

Jami’an tsaro sun ce sun kama wanda ake zargi kuma sun kwace tabaryar da ya yi amfani da ita wajen kaiwa mahaifiyarsa harin har ta mutu.

A cewar CSP Wakil, ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da Safiyanu a kotu da zarar an rundunar ta kammala tattara bayanan da take so.

Kara karanta wannan

Bauchi: Miji ya yi wa matarsa dukan tsiya har ta zarce lahira kan abincin Ramadan

Matashi ya bugawa mahaifinsa tabarya har lahira

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani matashi mai suna Ikechi ya jefa ƙaramar hukumar Obio Akpor, jihar Ribas cikin rudani da ya kashe mahaifinsa da taɓarya.

Wani ganau a garin Rumuaghaolu da abin ya faru, ya bayyana cewa matashin ya aikata wannan aika-aika ne bayan mahaifinsa ya ƙi ba shi wasu kuɗin da ya nema.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.