Ramadan: Dalibai Sun Fusata kan Rufe Makarantu a Arewa, NANS Ta Shirya Zanga Zanga

Ramadan: Dalibai Sun Fusata kan Rufe Makarantu a Arewa, NANS Ta Shirya Zanga Zanga

  • Kungiyar daliban kasar nan (NANS), ta bayyana takaicin rufe makarantu na mako biyar da gwamnatocin jihohin Arewa hudu suka yi
  • Jami'in hulda da jama'a na kungiyar, Samson Adeyemi ya ce sun ba gwamnonin Katsina, Kebbi, Kano da Bauchi wa'adin bude makarantun
  • Ya yi barazanar za su shiga zanga-zanga kan abin da ya kira tauye 'yancin dalibai na samun ilimi, musamman wadanda ba Musulmai ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kungiyar Dalibai ta Najeriya (NANS) ta yi barazanar gudanar da zanga-zanga a fadin kasar nan idan har ba a janye matakin rufe makarantu a wasu jihohin Arewa ba.

Kungiyar ta bukaci gwamnonin Bauchi, Katsina, Kano, da Kebbi da su janye hutun makarantu na mako biyar da aka bayar a cikin sa’o’i 72, idan ba haka ba za su dauki mataki.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi bayanin yadda bindigogi kusan 4,000 suka bace a karkashin kulawarta

Gwamnoni
NANS ta gargadi gwamnoni kan ba da hutun Ramadan Hoto: Abba Kabir Yusuf/Dr. Umaru Dikko Radda/Sen Bala AbdulKadir Muhammad
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun NANS na kasa, Samson Adeyemi, ya fitar a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta bayyana matakin rufe makarantu na mako biyar da gwamnonin suka dauka a matsayin tauye hakkin dalibai, musamman wadanda ba Musulmi ba.

NANS ta fusata da rufe makarantu

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa Adeyemi ya ce ba za su zura ido a cutar da daliban kasar nan ba, musamman Kiristoci da babu ruwansu da azumi.

Ya kara da cewa irin wannan mataki, idan ba a kalubalance shi ba, zai zama abin da zai kawo tangarda ga ilimi a fadin Najeriya.

Adeyemi ya ce:

"Kungiyar Dalibai ta Najeriya tana Allah-wadai da umarnin da gwamnonin Bauchi, Katsina, Kano, da Kebbi suka bayar na rufe makarantu a lokacin watan Ramadan."
"Wannan mataki ba wai kawai rashin adalci ba ne, har ma yana tauye hakkin dalibai na samun ilimi ba tare da tangarda ba."

Kara karanta wannan

Ramadan: CAN za ta yi shari'a da jihohin da suka rufe makarantu, ta kafa sharuda

"Rufe makarantu ya tauye hakkin dalibai," NANs

NANS ta jaddada matsayinta na kare hakkin kowane dalibi a Najeriya na samun ilimi, ba tare da la’akari da addininsa ba.

Daliba
NANS ta yi barazanar shiga zanga-zanga Hoto: Getty
Asali: Getty Images

Kungiyar ta ce rufe makarantu na tsawon lokaci saboda Ramadan zai kawo cikas ga ci gaban ilimi, tare da fifita addini fiye da hakkin daliban na samun ilimi.

Kungiyar ta ce:

"Dokar Najeriya da kuma yarjejeniyoyin kasa da kasa da Najeriya ke cikinsu sun tabbatar da ’yancin kowane dan kasa na samun ilimi.
Yanke hukuncin rufe makarantu saboda Ramadan ya sabawa wadannan dokoki, tare da kafa wata matsala da ke fifita addini fiye da hakkokin dalibai na samun ilimi."

Mai magana da yawun NANS ya kuma bai wa gwamnonin wa’adin sa’o’i 72 don janye wannan mataki, in ba haka ba za su fara gudanar da zanga-zanga a fadin Najeriya.

Ya kuma bukaci sauran masu ruwa da tsaki a fannin ilimi su hadu da kungiyar domin tabbatar da cewa hakkokin dalibai ba a take su ba.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamna ya rufe dukkanin makarantun jiharsa na tsawon mako 5

Gwamna ya ba da hutun makarantu

A wani labarin, mun kawo labarin cewa gwamnatin Bauchi ta umarci dukkanin makarantun dake fadin jihar da su tafi hutun mako biyar domin ba da damar azumtar Ramadana a gida.

Umarnin na kunshe a sanarwar da jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar ilimin Bauchi, Jalaluddeen Maina, ya fitar, ya ce hutun ya shafi makarantun firamare da sakandaren jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.