EFCC Ta Iza Keyar Tsohon Gwamna da Ɗansa zuwa Kotu, Ana Zargin Sun Wawure N47bn
- EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan Abia, Theodore Orji, da ɗansa Chinedum Orji kan zargin karkatar da kimanin Naira biliyan 47
- Hukumar ta gurfanar da tsohon gwamnan da wasu hudu, ciki har da tsohon kwamishinan kudi na Abia, Philip Nto, a gaban kotun jihar
- EFCC ta zargi wadanda ake tuhuma da sace kudin gwamnati da aka ware don tsaro, bashi, da ƙananan masana'antu, zargin da suka musunta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abia - Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia, Theodore Orji, da ɗansa, Chinedum Orji, da wasu mutum uku a gaban kotun jihar Abia.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da masu yi wa dukiyar al'umma zagon kasa, ta na zargin mutanen biyar da almundahanar kuɗin jama'a har N47bn.

Asali: Twitter
EFCC ta gurfanar da tsohon gwamna, mutum 4
Sauran wadanda ake tuhuma sun haɗa da Dr. Philip Nto, tsohon kwamishinan kudi na Abia, Obioma King, da Romas Madu, tsohon daraktan kudi na Abia, inji sanarwar EFCC a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gurfanar da su gaban Mai shari'a Lilian Abai, a kan tuhume-tuhume 16 da suka haɗa da haɗin baki, sata, da wawure kuɗaɗen gwamnati da aka ware don ayyukan jama'a.
EFCC ta zargi wadanda ake tuhuma da aikata laifuffuka masu yawa na kudi, ciki har da almundahanar N22.5bn da aka ware a matsayin kudin tsaro tsakanin 2011 zuwa 2015.
Laifuffukan EFCC ta ke zargin sun aikata
An kuma zarge su da wawure N13bn daga kudin bashin Diamond Bank, da kuma karkatar da N12bn daga kudin bashin Paris Club da aka ba jihar.
Bugu da ƙari, EFCC ta ce wadanda ake tuhuma sun yi sama da fadi da N10.5bn da aka karbo rance daga bankin FBN don amfanin jihar Abia da kananan hukumominta.

Kara karanta wannan
Tsohon shugaba Buhari, El-Rufa'i da sauran jagororin APC sun ki halartar taron APC
Rahoton ya kuma nuna cewa ana zargin su da satar N2bn daga kudaden Bankin CBN da aka ware don bunkasa ƙananan masana'antu (SMEs).
Wadanda ake zargi sun musanta tuhumar

Asali: Twitter
A lokacin sauraron shari'ar, lauyan EFCC, Farfesa Kemi Pinheiro, SAN, ya roki kotu ta karanta wa wanda ake tuhuma ƙarin bayani kan tuhumar da ake musu.
Sai dai bayan karanta masu laifuffukan da ake tuhumarsu da su, tsohon gwamnan, dansa da sauran mutanen uku sun musanta aikata dukkanin laifuffukan.
Lauyoyin da ke kare wadanda ake tuhuma, ciki har da Bode Olanipekun, SAN (lauyan wanda ake tuhuma na farko) da Chikaosulu Ojukwu, SAN (na biyu).
Sauran lauyoyin sun hada da K.I. Oleh, Esq., Okey Amechi, SAN, da Isaac Anya, Esq., kuma sun gabatar da buƙatar a bayar da belin wadanda suke karewa.
Hukuncin farko da kotu ta yanke
Lauyan masu kara bai nuna adawa da da buƙatar bayar da belin ba, amma ya roki kotu da ta yi amfani da iko wajen sanya sharrudan belin.
Bayan ɗan lokaci na hutu, Mai shari'a Abai ta amince da bayar da belin wadanda ake tuhuma, sannan ta dage shari'ar zuwa ranar 18 da 19 ga Yuni, 2025.
Badakalar N27bn: EFCC ta gayyaci Theodore Orji
A wani labarin, mun ruwaito cewa, EFCC gayyaci tsohon gwamnan Abia, Sanata Theodore Orji, zuwa ofishinta domin amsa tambayoyi game da zargin almundahanar N27bn.
Majiya ta bayyana cewa an gayyace shi ne sakamakon korafe-korafen rashawa da aka rika shigarwa a kansa tun bayan saukarsa daga kujerar gwamna a 2015.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng