Almundahar N27bn: EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan Abia

Almundahar N27bn: EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan Abia

Rahoton da muka samu daga Punch ya nuna cewa hukumar yaki da rashawa EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Theodore Orji zuwa ofishinta domin amsa tambayoyi kan zargin almundahar N27 biliyan yayin da ya ke gwamna.

An gano cewar gwamnan da ya mulki jihar daga 2005 zuwa 2015 ya isa ofishin EFCC da ke Abuja tare da lauyansa sanya da kaya mai launin ruwan madara mai dogon hannu da aka kira da 'sanata'

Majiyar Legit.ng ta gano cewa EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan ne sakamakon korafe-korafe da aka rika shigarwa a kansa bayan ya sauka daga kujerar gwamna a 2015.

Almundahar N27bn: EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan PDP domin amsa tambayoyi
Almundahar N27bn: EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan PDP domin amsa tambayoyi
Asali: Twitter

Cikin tuhumar da ake masa sun hada da karkatar da biliyoyin kudi da babban bankin Najeriya CBN ta bawa jihar Abia domin tallafawa masu kananan sana'o'i da kamfanoni tare da zarginsa da karkatar da kudade da aka ware domin yaki da kwararowar hamada da wasu iftila'i a jihar.

DUBA WANNAN: Zan biya N50,000 mafi karancin albashi - Dan takarar shugaban kasa

Ana kuma zargin cewa tsohon gwamnan ya karkatar da kudade daga cibiyar cigaban jihohin da ke samar da man fetur wanda gwamnatin tarayya ta kafa domin gudanar da ayyukan more rayuwa ga al'ummar jihohin da ake hakar man fetur.

Orji ya yi amfani da kudaden wajen saya filaye da gidaje a Abia, Port harcourt da Abuja wanda aka tsamanin EFCC za ta kwace wasu daga cikinsu.

An kuma ruwaito cewa an gayyaci jami'ai daga CBN, ofishin Alkalin Alkalai na kasa, Bankunan yan kasuwa da wasu hukumomin domin su bayar da sheda a kan binciken da EFCC ke gudanarwa a kansa Sanatan.

Kakakin hukumar EFCC na rikon kwarya, Mr Tony Orilade bai amsa wayarsa ba aka kira shi sai dai ya aike da sakon kar ta kwana inda ya ce, "Eh, da gaske ne tsohon gwamnan jihar Abia ya zo ofishin mu.

"Amma ba zan iya bayar da wani bayani a yanzu ba. Idan lokacin gurfanar da shi a kotu ya yi, za mu sanar da manema labarai."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel