Kudin tsaro: Theodore Orji ya batar da N38.8 a lokacin da ya ke gwamnan Jihar Abia

Kudin tsaro: Theodore Orji ya batar da N38.8 a lokacin da ya ke gwamnan Jihar Abia

Tsohon gwamna Theodore Orji ya yi wa hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa bayanin yadda ya kashe kudin tsaro a lokacin da ya ke mulki.

Sanata Theodore Orji ya bayyana cewa a cikin shekaru takwas da ya yi ya na mulki a jihar Abia, ya kashe Naira biliyan 38.8 da ake warewa mutanensa domin inganta harkar tsaro.

Orji wanda ya yi mulki tsakanin 2007 da 2015 ya na hannun EFCC ne inda ake zarginsa da wawurar Naira biliyan 48. Sanatan mai-ci ya musanya wannan zargi da ake yi masa.

Sanatan na Abia ta tsakiya, ya ce ya raba wannan Biliyan 38.8 ne tare da ‘yan majalisar dokoki, da jami’an tsaro, da kuma sarakunan gargajiya da ke mulki a fadin jiharsa ta Abia.

Jaridar The Sun ta rahoto yadda tsohon gwamnan ya ke ikirarin ya batar da wadannan makudan kudi. Ya ce jami’an NSCDC su kan samu kaso kai tsaye daga cikin kudin tsaron jihar.

KU KARANTA: Gwamnan Katsina ya sassauta takunkumin kulle na mako guda

Kudin tsaro: Theodore Orji ya batar da N38.8 a lokacin da ya ke gwamnan Jihar Abia
Theodore Orji Hoto daga: ICIR
Asali: Twitter

‘Yan majalisar jihar Abia su kan tashi da Naira miliyan 60 duk wata na tsawon shekaru takwas da ya yi ya na mulki. ‘Yan majalisar dokoin Abia sun samu Naira biliyan 5.760 inji Orji.

Tsohon gwamnan na jam’iyyar PDP ya kuma shaidawa jami’an EFCC cewa ya kan biya Naira miliyan 75 duk wata ga wadanda su ke bankado masa sirrin tsaro a cikin jihar Abia.

A cewar Orji, duk watan Duniya ya kan biya wadannan mutane da bai bayyana sunayensu ba miliyoyi har ya sauka daga ofis. Haka zalika jami’an tsaro su kan tashi da miliyoyi.

A 2007, Orji ya karbi Naira miliyan 370 da sunan tsaro, tsakanin 2008 da 2015 kuma jihar Abia ta na samun Naira miliyan 410 duk wata wanda EFCC ta ke ganin an yi awon gaba da su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng