Jama'a Suna Zaman Ɗar Ɗar, Jami'an Tsaro da Sulken Yaki Sun Kewaye Gidan Sarki a Kano

Jama'a Suna Zaman Ɗar Ɗar, Jami'an Tsaro da Sulken Yaki Sun Kewaye Gidan Sarki a Kano

  • Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana cewa an samu rahoton sirri bisa shirin wasu 'yan daba na tayar da hatsaniya da hankulan mazauna jihar
  • Wannan na kunshe a sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fiyar bayan jibge jami'an tsaro a jihar
  • Jama'a sun fara ganin jami'an tsaron sanye da kaya irin na yaki, da fuskokinsu a rufe suna ba gidan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero kariya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Hukumomin tsaro da suka hada da na yan sanda da kuma sojoji sun tare hanyar zuwa fadar gwamnatin Kano musamman daura da gidan Nasarawa da sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero yake zaune.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaba Buhari, El-Rufa'i da sauran jagororin APC sun ki halartar taron APC

A safiyar yau dai an sake tsaurara tsaro tare da jibge tawagar hukumomin tsaron baya ga rufe wasu daga cikin hanyoyin da za su sada da gidan sarki na Nasarawa.

Jihar
Jami'an tsaro sun harba borkonon tsohuwa a kan titin gidan gwamnatin Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Rundunar yan sandan Kano ta tabbatar da lamarin a sanarwar da kakakinta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Yadda jama’a suka rika zaman fargaba

Wasu mazauna Kano da suka bi titin gwamnati a wannan rana sun shaidawa Legit cewa sun cika da mamakin ganin dakarun sojojin dauke da mugayen makamai sun rufe titin.

Wani mai adaidaita sahu ya fito daga cikin gari ya bayyana yadda ya rika zagaye da fasinjan unguwar Hotoro, a kokarin kaucewa ido biyu da dakarun.

Ya ce:

“Da muka sauko ta kan gada na gansu, sai muka koma ta titin Obasanjo, na bi wasu lunguna har muka koma ta titin Kawo.”

Wani Ibrahim Aminu Rimin Kebe ya ce sai da ya taka a kafarsa daga kan titin gidan gwamnati har zuwa ‘farm centre,’ domin ana barin daidaikun mutane su wuce.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ɓullo da sabuwar dabara, mataimakin ciyaman ya faɗa tarko a Zamfara

Dalilin jibge jami'an tsaro a Kano

A sanarwar da SP Kiyawa ya fitar, ya bayyana cewa sun samu rahotannin sirri kan cewar matasan sun shirya gudunar da wata zanga-zangar lumana.

Jihar
'Yan sanda sun kama 'yan daba a Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Sai dai ya bayyana cewa an samu tabbacin zanga-zangar za ta haifar da hatsaniya da kuma tayar da hankulan mazauna jihar.

Rundunar sandan Kano ta yi kame

Kakakin 'yan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da cewa, sun samu nasarar kama mutane 17 wadanda ake zargin su da hannu wajen shirya zanga-zanga.

Rundunar yan sandan Kano ta tabbatar da cewa, a shirye take a ko wane lokaci domin dakile duk wata barazana ta rashin tsaro a lungu da sako dake fadin jihar nan.

SP Abdullahi Kiyawa, yayi kira ga al’umma da su ci gaba da ba wa hukumomin tsaro hadin kan da ya kamata ta hanyar ba su rahotanni sirri.

An samu zanga-zanga a Kano

Kara karanta wannan

Shirin babban taron APC ya gama kankama, jagororin jam'iyya sun hallara Abuja

A wani labarin, kun ji cewa an samu wata zanga-zanga ta barke a gaban fadar Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, lamarin da ya sa aka samar da tarin jami'an tsaro don ba da kariya.

Jami'an tsaro da suka haɗa da ƴan sanda da DSS sun ɗauki matakin tarwatsa masu zanga-zangar ta hanyar sanya musu barkonon tsohuwa, lamarin da ya kara jefa tsoro a zukatan jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.