Matakin da Sojoji Suka Dauka da Bello Turji Ya Sanya N25m a Kauyukan Sokoto
- Mazauna Sokoto sun samu umarni daga rundunar soji da kada su biya harajin N25m da Bello Turji ya kakaba musu, domin za a kare su
- Manjo Janar Onumajuru ya ce Turji ya tsere tun bayan farmakin da sojoji suka kai masa a Zamfara, kuma ana bin sawunsa don kashe shi
- Rundunar soji ta bukaci al’ummomi da su yi watsi da bukatar biyan kudi ga ‘yan bindiga, domin sojoji na aiki don tabbatar da tsaronsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hedikwatar tsaron Najeriya ta bukaci mazauna kauyukan jihar Sokoto da su yi watsi da biyan harajin N25m da Bello Turji ya kakaba masu.
Rundunar ta tabbatar wa mazauna yankin cewa za ta kare su, inda ta bukace su da kada su firgita da barazanar da Turji ke yi, domin nan ba da jimawa ba sojoji za su kama shi.

Asali: Twitter
Babban jami’in ayyukan tsaro, Manjo Janar Emeka Onumajuru, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bayyana cewa Turji ya tsere daga jihar Zamfara tun bayan wani farmakin sojoji da aka kai masa a watan Janairu.
Saboda haka ne ma sojojin suka kira shi da 'matsoraci' bayan ya gudu ya bar dansa da mayakansa a lokacin artabu da dakarun tsaro.
Bello Turji ya kakabawa mazauna Sokoto haraji
Legit Hausa ta rahoto dan majalisar Sokoto mai wakiltar karamar hukumar Sabon Birni, Aminu Boza, ya shaida wa manema labarai cewa Turji ya sake bayyana a jihar Sokoto kuma ya kakaba wa wasu kauyuka harajin N25m.
Hon. Aminu Boza ya kara da cewa Bello Turji ya kafa sansani a cikin dajin da ke yankin karamar hukumar Isa.

Kara karanta wannan
Karya ta kare: Sojoji sun gano maboyar Bello Turji, sun fadi lokacin kawar da shi
To amma a ranar Litinin, Manjo Janar Onumajuru ya bayyana cewa rundunar soji ba za ta yi wasa da lamarin Turji ba, inji rahoton Punch.
Ya shawarci mazauna yankin da kada su yarda su biya wani nau’in kudin kariya ga ‘yan bindiga, yana mai jaddada cewa sojoji na bakin aiki don kare su.
'Ka da ku biyan harajin Turji' - Sojoji ga Sakkwatawa

Asali: Twitter
Manjo Janar Onumajuru ya shaida cewa:
“Dangane da batun Bello Turji da ke kakaba wa mutane haraji, na riga na fada cewa muna aiki tukuru don kare al’ummomin da ke cikin hadari.
“Abin da muke bukata shi ne al’ummomi su yarda cewa rundunar soji na kare su. Idan suka yarda da hakan, to babu bukatar amincewa da duk wata bukatar kudin fansa ko kariya, domin muna nan don kare su.
“Ina kira ga al’ummomi ta wannan kafar, kada ku amince da biyan kudin kariya a kowane irin nau’i, domin muna da dakarun da ke tabbatar da tsaro a gonaki da kuma ba da damar kowa ya ci gaba da harkokinsa na yau da kullum.
An cafke mai sayarwa Bello Turji makamai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an tsaro a jihar Sokoto, sun cafke Hamza Suruddubu, wanda ake zargi da samar da makamai ga dan bindiga Bello Turji.
Rahotanni sun nuna cewa Suruddubu na safarar makamai daga Zamfara zuwa Gabashin Sokoto, inda yake sayarwa manyan ‘yan ta’adda, ciki har da Halilu Buzu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng