Gwamnan Sakkwato Ya Waiwayi Malaman Musulunci, An Yi Masu Tanadin Ramadan
- Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato ya kaddamar da shirin tallafin watan Ramadan domin rage wa malamai radadin rayuwa
- Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an dauki matakin raba tallafin ne domin karfafa wa malaman gwiwa wajen aikin Allah SWT
- An raba malaman zuwa rukuni–rukuni, wasu sun samu N200,000 da buhunan masara biyar, wasu za su samu abin da ya haura haka
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto – Gwamnan Jihar Sakkwato, Dr. Ahmed Aliyu, ya kaddamar da shirin tallafin Ramadan na shekarar 2025, wanda aka shirya domin rage wa al’ummar Musulmi wahalhalun da suke fuskanta.
Shirin ya kunshi rabon buhunan masara da kuma tallafin kuɗi ga malamai, limaman masallatan Juma’a, mataimakansu, ladanai da wasu kungiyoyin addini dake fadin jihar.

Kara karanta wannan
Mai alfarma sarkin musulmi ya aika saƙo ga malamai ana shirin fara azumin Ramadan

Asali: Twitter
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan a kan kafafen sadarwa na zamani, Naseer Bazza, ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Sakkwato za ta raba tallafi ga malamai
Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana cewa kowanne Limamin Masallacin Juma’a zai karɓi buhunan masara guda biyar tare da tallafin kuɗi na N100,000.
Haka nan, Na’ibai za su karɓi buhunan masara guda uku da kuma N50,000, yayin da ladanai za su samu buhunan masara guda biyu da kuma N50,000.

Asali: Twitter
Gwamnatin jihar za ta ba wa manyan malamai 300 tallafin kuɗi na N200,000 kowannensu, domin ƙarfafa musu gwiwa a hidimarsu ta addini.
Har ila yau, wasu malamai 100 za su samu N100,000 kowannensu, a matsayin girmamawa ga gudunmawar da suke bayarwa wajen ilmantar da al’umma a jihar.
Sannan malamai 10 daga kowane gunduma a cikin kananan hukumomi 23 na jihar za su karɓi N50,000.
Dalilin gwamnatin Sakkwato na rabon tallafi
Gwamnatin Sakkwato ta bayyana cewa an shirya ba da tallafin ne domin ƙarfafawa malamai su ci gaba da gudanar da aikinsu na addini tare da rage musu wahala a lokacin azumin Ramadan.
Haka nan, gwamna Ahmed Aliyu ya sanar da cewa kungiyoyin addini 150 a fadin jihar za su samu tallafin kuɗi na N300,000.
Ya ce an dauki matakin ne domin mutuntawa da kara karfin gwiwa a kan irin rawar da suke takawa wajen bunƙasa addinin Musulunci a jihar.
Gwamnatin Sakkwato ta bude katafaren masallaci
A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayyana shirin ta na faɗaɗa shirin ciyarwa a watan Ramadan domin tallafawa mabukata da marasa galihu a faɗin jihar.
Gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu, ne ya sanar da hakan yayin da yake ƙaddamar da masallacin Juma’a na Ruggar Wauru, wanda aka gyara a Sakkwato.
A cewar Gwamna Aliyu, gwamnati ta fara shiri tun da wuri domin gudanar da azumin Ramadan na 2025 cikin sauƙi, tare da ƙara yawan abincin da ake rabawa a wuraren ciyarwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng