Gidauniya Ta Dauko Babban Aiki, Za Ta Gina Muhimmin Titi da Ya Haɗa Jihohin Arewa 2
- Wata Gidauniya ta kudiri aniyar taimakawa al'ummar yankin Kampani da ke jihar Kebbi a Arewacin Najeriya
- Gidauniyar Sameer Salihu ta fara gyaran hanyar Kampani a ƙaramar hukumar Argungu don sauƙaƙa wa matafiya da ke jigila
- Shugaban Gidauniyar, Sameer Salihu Argungu ya ɗauki nauyin aikin ne don tallafawa ayyukan Gwamna Nasir Idris da al'umma domin jin daɗinsu
- Gidauniyar na da manufofi kamar koyar da matasa sana'o'in hannu, bayar da jari, da samar da hasken fitila mai amfani da hasken rana a yankunan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Argungu, Kebbi - Bayan daukar lokaci mai tsawo ba tare da hanya ba, Gidauniya ta shirya gyaran titi a jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya.
Gidauniyar Sameer Salihu ta fara aikin gyaran hanyar kauyen Kampani da ke karamar hukumar Argungu a jihar.

Asali: Facebook
Gidauniya ta shiga aikin gwamna, za ta yi titi
Jami'in hulda da jama'a da bangaren sadarwa a Gidauniyar, Ashiru Musa Argungu shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa a tattaunawarsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ashiru ya ce Gidauniyar karkashin jagorancin shugabanta, Sameer Salihu Argungu, ta fara gyaran hanyar da ta haɗa jihar Kebbi da Sokoto.
Ya ce hanyar tana garin da ake kira Kampani da ke karamar hukumar Argungu wanda aka shirya gyarawa don sauƙaƙa wa matafiya.
Musabbabin lalacewar babbar hanyar a Kebbi
Ashiru ya fadawa wakilin Legit Hausa cewa:
"Akwai wata hanya da ta haɗa Sokoto zuwa Kebbi, akwai wani kauye da ake kira Kampani.
"Ruwan da aka yi kasan an samu barazana musamman nan Kebbi ya ci wurare da dama, da ruwan ya zo ya ci wurare da gidaje da yawa da kuma babbar hanyar da ta haɗa Sokoto zuwa Kebbi a nan kauyen kenan.
"Yanzu Gidauniyarmu ta dauki nauyin gyaran hanyar har an fara aikin yanzu haka da muke magana da kai."

Hanyoyin da Gidauniyar ke ba da gudunmawa
Gidauniyar ta ba da umurnin gyaran hanyar da aka fara tun tuni inda motoci da ma'aikata suka fara aiki a halin yanzu ba tare da bata lokaci ba.
Sanarwar ta ce Gidauniyar ta yi haka ne domin tallafawa ayyukan alheri da ragewa gwamnatin Dakta Nasir Idris dawainiya da raya al'ummar jihar da yake yi a jihar ba dare ba rana.
Daga cikin kudurorin gidauniyar akwai koyar da matasa sana’o’i, bayar da jari, da saka fitila mai amfani da hasken rana a wurare daban-daban a yankin Argungu.
Gidauniya ta tallafawa ɗalibai da littattafai a Bauchi
A baya, mun kawo labarin cewa Gidauniyar Ibrahim Ali Usman ta tallafawa ɗalibai da littattafai domin inganta harkokin ilimi a jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan
Ministan tsaro ya yi albashir ga Arewa kan matsalar ta'addanci, ya tabo alaka da Nijar
Gidauniyar ta ƙaddamar da tallafin litattafai akalla 1,050,000 ga yara da mata dalibai domin tallafa musu a yankin Bauchi ta Kudu a wani babban taro a jihar.
Shugaban Gidauniyar, Hon. Ibrahim Ali Usman ya bayyana cewa 'Ibrahim Ali Usman Foundation' za ta cigaba da tallafawa ilimi a jihar musamman mata da yara.
Asali: Legit.ng