Karya Ta Kare: Sojoji Sun Gano Maboyar Bello Turji, Sun Fadi Lokacin Kawar da Shi

Karya Ta Kare: Sojoji Sun Gano Maboyar Bello Turji, Sun Fadi Lokacin Kawar da Shi

  • Ƙarshen ta'addancin hatsabibin ɗan bindiga Bello Turji, ya kusa zuwa bayan dakarun sojoji sun gano inda yake
  • Rundunar sojoji ta ba da tabbacin nan ba da jimawa ba za a kawar da Bello Turji wanda ya addabi mutanen Zamfara da sauran jihohin makwabta
  • Sojojin sun buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri domin bibiyar hatsabibin ɗan bindiga aiki ne mai wahalar gaske

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta sake taɓo batun hatsabibin ɗan bindiga, Bello Turji.

Rundunar sojojin ta ba da tabbacin cewa ana bibiyar Bello Turji, kuma za a kawar da shi nan ba da jimawa ba.

Sojoji sun durfafi Bello Turji
Sojoji sun ba da tabbacin kawar da Bello Turji Hoto: @ZagazolaMakama, @DefenceInfo
Asali: Twitter

Babban daraktan ayyuka a hedkwatar tsaro (DHQ), Manjo Janar Emeka Onumajuru, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a tashar Channels tv a shirinsu na 'The Morning Brief' a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun dira kan mutanen gari, an samu asarar rai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun gano inda Bello Turji ya ɓoye

Manjo Janar Onumajuru ya bayyana cewa rundunar sojoji tana da masaniya kan inda Bello Turji yake a halin yanzu, amma ba zai yi ƙarin bayani ba.

"Da farko, ina so ku sani cewa babu wata tattaunawa ko sulhu tsakanin Bello Turji da sojojin Najeriya."
"A yanzu da nake magana, Bello Turji yana ɓoye, ya na ci gaba da ɓoyewa, kuma rundunar soji tana bibiyarsa. Rundunar sojoji na ci gaba da bibiyarsa kuma nan ba da ɗaɗewa ba za a kawar da shi."

- Manjo Janar Emeka Onumajuru

Ya roƙi ƴan Najeriya da su riƙa yi wa rundunar sojoji uzuri domin bibiyar hatsabibin ɗan bindiga abu ne wanda ke ɗaukar dogon lokaci.

Sai dai ya tabbatar da cewa ba za a ɗauki lokaci mai tsawo ba kafin a kawar da Bello Turji, domin kawo ƙarshen ayyukansa a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Zuwan hafsan sojoji ya kawo alheri, ya yi wa dakaru albashir bayan kara alawus

'Ka da ku biya Bello Turji haraji' - Onumajuru

A makon da ya gabata wani ɗan majalisar jihar Sokoto, Aminu Almustapha Boza, ya tabbatar da kasancewar Bello Turji a ɗaya daga cikin dazuka da ke ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Dan majalisar, wanda ke wakiltar ƙaramar hukumar Sabon Birni a majalisar dokokin jihar Sokoto, ya bayyana cewa Bello Turji yana karɓar haraji daga hannun jama’ar yankin.

Sai dai Manjo Janar Onumajuru ya bukaci al’ummar Sokoto da su yi watsi da barazanar Bello Turji, kuma su daina biyan harajin da yake karɓa, yana mai tabbatar musu da cewa rundunar sojoji za ta kare su.

“Don haka, ina kira ga jama'a ta wannan kafar, ka da ku amince da duk wata buƙatar biyan kuɗin kariya a kowane irin yanayi, domin muna da sojoji da ke tabbatar da tsaro a gonaki domin gudanar da harkoki na yau da kullum."

Kara karanta wannan

Jirgin sojoji ya faɗo kan gidajen mutane, Janar da wasu sama da 40 sun mutu

- Manjo Janar Emeka Onumajuru

Wani mazaunin jihar Zamfara mai suna Jamilu Abdullahi ya bayyana cewa ya kamata sojoji su yi da gaske wajen kawar da Bello Turji.

"Sojoji sun daɗe suna cewa sun kusa kawo ƙarshen ɗan ta'addan nan amma har yanzu shiru kake ji. Ya kamata su nuna da gaske suke yi."
"Bai kamata a ce an bar shi ya ɗauki tsawon lokaci yana cin karensa babu babbaka ba."

- Jamilu Abdullahi

Jami'an tsaro sun cafke mai sayarwa Turji makamai

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun samu nasara a ƙoƙarin da suke yi na kawo ƙarshen ayyukan hatsabibin ɗan bindiga, Bello Turji.

Jami'an tsaron sun samu nasarar cafke Hamza Suruddubu wanda yake sayarwa Bello Turji makamai a ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng