'Yan Bindiga Sun Harbi Malamin Addini, Sun Sace Mutum 6 Suna Tsaka da Yin Ibada
- 'Yan bindiga sun farmaki coci a Delta inda suka harbi fasto tare da sace mutum shida, ciki har da masu gadi biyu, yayin taron ibadar dare
- Matar faston ta bayyana cewa maharan sun bude wuta, lamarin da ya sa mijinta ya rasa yatsunsa biyu bayan harsashi ya samu kafarsa
- Sai dai, Fasto Steve Victor ya ce tun bayan harin ba a karɓi kira daga masu garkuwa ba, amma jami’an tsaro na kokarin kubutar da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Delta - 'Yan bindiga sun farmaki cocin Elyon Paradise Ministry da ke Ogwashi-Uku, Delta, yayin taron ibada a daren Juma’a, inda suka harbi fasto tare da sace mutum shida.
An kai harin ne da misalin karfe 10 na dare, kusa da kwalejin jihar Delta, inda suka harbi Apostle Divine Omodia, wanda yanzu yake kwance a asibiti bayan jin raunuka.

Kara karanta wannan
An yi arangama a Niger, dan sanda ya dirkawa jami'ar hukumar NIS bindiga, an tsare wasu

Asali: Getty Images
Delta: 'Yan bindiga sun harbi fasto
Wannan farmakin ya haifar da fargaba a yankin, inda mazauna garin ke kira ga hukumomi da su dauki matakin gaggawa domin kubutar da wadanda aka sace, inji Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matar faston, Faith Omodia, ta bayyana yadda lamarin ya faru, tana mai cewa maharan sun bude wuta ba kakkautawa cikin dakin ibadar.
“Ina kwance da jaririna a dakin cocin, sai na ji harbe-harbe. Kafin mu ankara, harsasai sun fara shigowa cikin ginin,” in ji Faith.
'Yan bindigar sun sace mutane shida
Ta ce 'yan bindigar, sun harbi mijinta, Apostle Divine a kafarsa, lamarin da ya kai ga har ya rasa yatsunsa biyu sakamakon harbin.
Faith ta ce:
"Bayan sun bude wuta, 'yan bindigar sun tarwatsa masu ibada, sannan suka tafi da mutum shida, ciki har da masu gadin cocin biyu."
An bayyana sunayen wadanda aka sace kamar haka: Helen Onwuamaeze, Ariyo Emmanuel, Chike Okolo, da Blessing Waye, tare da wasu masu gadi da ba a bayyana sunayensu ba.
Fasto ya fadi kokarin da 'yan sanda ke yi

Asali: Twitter
Wani fasto na cocin, Steve Victor Onuchukwu, ya fadawa jaridar The Guardian cewa tun bayan harin, masu garkuwar ba su tuntubi kowa ba domin neman kudin fansa.
Ya ce an riga an shigar da rahoton lamarin ga 'yan sanda, amma har yanzu ba a sami sakamako mai kyau ba.
Sai dai Steve Victor Onuchukwu ya ce wani jami’in tsaro ya sanar da shi cewa ana aiki tukuru domin ganin an kubutar da su.
'Yan sanda sun ce basu da labari
Har ila yau, akwai fargaba kan lafiyar Apostle Omodia, wanda aka yi wa tiyata a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba, inda likitoci ke kokarin ceton rayuwarsa.
"Mun garzaya da shi asibiti. A halin yanzu yana cikin dakin tiyata, likitoci na kokarin tabbatar da cewa an ceto rayuwarsa," in ji Onuchukwu.
A halin yanzu, rundunar 'yan sandan Delta ba ta tabbatar da afkuwar lamarin ba.
Da aka tuntube shi, kakakin rundunar, Bright Edafe, ya ce: “Babu wani rahoto da aka kai wa ‘yan sanda kan wannan harin.”
'Yan bindiga sun kashe fato, sun sace 19
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai farmaki a Jihar Neja, inda suka kashe wani fasto tare da yin garkuwa da akalla mutane 19 kafin su tsere.
Kamar yadda suka saba kai hare-hare a kauyuka, sun kutsa cikin garuruwan Ogu da Tegina da ke Karamar Hukumar Rafi dauke da babura masu yawa.
Asali: Legit.ng