Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace mutum 19, sun halaka fasto a Niger
- 'Yan bindiga sun afka wa jihar Neja, yanzu haka sun kashe wani fasto sannan sun yi garkuwa da a kalla mutane 19
- Kamar yadda suke shiga kauyaku, sun shiga garin Ogu da Tegina da ke karamar hukumar Rafi a baburansu da yawa
- Sun isa tsakar dare, inda suka yi ta harbi a sama, akwai gidan da suka shiga har kicin suka kwashi girki kafin su cigaba da ta'addanci
'Yan bindiga sun yi garkuwa da a kalla mutane 19 a garin Ogu da Tegina da ke karamar hukumar Rafi a jihar Neja.
Shugaban ma'aikatan shugaban karamar hukumar Rafi, Mohammed Mohammed, ya tabbatar wa da gidan talabijin din Channels faruwar lamarin a ranar Litinin.
Har kiran wasu daga cikin mazauna unguwannin don samun karin bayani a kan al'amarin, Channels TV ta wallafa.
An yi kokarin ji daga bakin jami'in hulda da jama'a na Neja, Wasiu Abiodun, amma al'amarin ya faskara, don bai dauki wayar ba kuma bai bayar da ansar sakon da aka tura masa ba.
Wani mazaunin Ogu, Kamal Wayam, ya koka a kan yadda 'yan bindigan suka afka wa garin a ranar Lahadi suka fara harbi a sama.
KU KARANTA: Birtaniya ta garkame faston Najeriya da ya shahara a gagarumar damfarar 'ilimi'
"Yan bindigan sun isa da yawansu zuwa Ogu a kan baburansu kafin mu ankara, har sun fara harbi a sama.
"Sun tattara mutane daga cikin gidajensu, sannan suka kwashe duk wasu kayan alatu, suka yi awon gaba dasu," kamar yadda Wayam ya fadi yayin tattaunawa da Mohammed.
Ya kara da cewa, "Sun kwashi mutane 6 daga Ogu, 4 daga cikinsu duk 'yan gida daya ne, yayin da sauran 2 kuma baki ne."
Ogu wani gari ne da ke kusa da Wayam wani gari mai nisan kilometers 2 daga Kagara, hedkwatar karamar hukumar Rafi.
KU KARANTA: Hotunan sojin Najeriya suna tsaro da taya manoman Zabarmari girbi a gona
Sannan sun kai harin garin Tegina da misalin 12:30am na ranar Litinin, inda suka kwashi mutane 16. Da suka shiga wani gida, har zama suka yi a kicin suka cinye musu abinci tas.
Bayan harin da kwana 4 suka saci wani shugaban matasan APC, dagacin kauyen Gunna, da yaran wasu ma'aikatan lafiya guda 2 da ke aiki a Garin Gabbas a karamar hukumar.
Sannan sun kashe wani faston ECWA, Jeremiah Ibrahim a anguwar Chukuba da ke karamar hukumar Shiroro. Sun kashe shi bayan yaje gonarsa sai ya biya wurin abokinsa, inda aka kashe shi.
A wani labari na daban, har yanzu ba a ga dalibai 668 na makarantar sakandaren gwamnati ta kimiyya da ke Kankara ba, kamar yadda rajistar makarantar ta nuna.
Daya daga cikin wakilanmu, wanda ya ziyarci makarantar jiya ya tattara bayanai akan yadda al'amarin ya faru, ya ce makarantar tana da dalibai 1,074 a manya da kananun azuzuwanta.
Wata majiya ta ce, "A bangaren kananun azuzuwa, akwai azuzuwa 6, JSS 1A, mai dalibai 58, 1B, mai dalibai 62 da 1C, mai dalibai 64; jSS 2A mai dalibai 74, 2B mai dalibai 79 da 2C mai dalibai 75."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng