Tinubu Ya Amince a Kafa Sababbin Jami'o'in Tarayya a Wasu Jihohi 2, An Fadi Sunaye

Tinubu Ya Amince a Kafa Sababbin Jami'o'in Tarayya a Wasu Jihohi 2, An Fadi Sunaye

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa Jami’ar Fasaha a Iyin Ekiti da Jami’ar Noma a Iragbiji don inganta ilimi da noma a Najeriya
  • Jami’ar Iyin Ekiti za ta mayar da hankali kan fasahar zamani, injiniyanci da kimiyyar muhalli don samar da sabbin hanyoyin ci gaba
  • Jami’ar Iragbiji za ta bunkasa noma, horas da kwararru, inganta dabarun samar da abinci, da tallafa wa ci gaban tattalin arzikin yankin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da dokokin da suka kafa sababbin jami’o’in tarayya biyu a Najeriya.

Jami’o’in da aka kafa sun hada da Jami’ar Fasaha da Kimiyyar Muhalli, Iyin Ekiti da Jami’ar Noma da Nazarin Ci Gaba, Iragbiji, Osun.

Shgaban kasa Bola tinubu ya rattaba hannu kan dokokin kafa jami'o'i biyu a Osun da Ekiti
Tinubu ya amince a kafa jami'o'i biyu a jihohin Osun da Ekiti. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya bayyana amincewa da dokokin a Abuja, a ranar Alhamis, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar dattawa ta amince da kudirin dokokin a 2023 da 2024, inda suka samu amincewar majalisar wakilai kafin Shugaba Tinubu ya sanya hannu.

Jami’o’in za su inganta ci gaban Najeriya

Sanata Bamidele ya ce sababbin jami’o’in za su taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban kasa, musamman a fannin fasaha, noma da kare muhalli.

“Ayyukan jami’o’in za su cike gibin ilimi a fannin kimiyya da fasaha, da habaka noma don tabbatar da wadatar abinci a Najeriya,” inji shi.

Ya bayyana amincewar Tinubu da dokokin a matsayin wani mataki mai muhimmanci da zai taimaka wajen shawo kan matsalar karancin abinci da dumamar yanayi.

Gwamnatin tarayya ta goyi bayan sababbin jami’o’in

Ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya ba da shawarar kafa jami’o’in a wata wasika da ya aika wa fadar shugaban kasa a ranar 19 ga Fabrairu.

Ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa ya yi magana kan jami'o'in da aka amince a kafa
Ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa ya magantu kan amincewar Tinubu na kafa sababbin jami'o'i. Hoto: @DrTunjiAlausa
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa Jami’ar Fasaha da Kimiyyar Muhalli, Iyin Ekiti, za ta mayar da hankali kan ilimi da bincike mai dogaro da fasaha.

Kara karanta wannan

NNPP ta yi babban rashi, ƙusa a jam'iyyar Kwankwaso ya koma APC

“Za ta samar da kwararru a fannin injiniyanci, kirkire-kirkiren fasaha da kimiyyar zamani domin bunkasa masana’antu da samar da ayyukan yi,” inji ministan.

Haka kuma, jami’ar za ta rungumi nazarin muhalli da mayar da hankali kan sauyin yanayi, makamashi mai tsafta, da cigaban birane masu dorewa.

Jami’ar Iragbiji za ta taimaka wajen wadatar abinci

Dangane da Jami’ar Noma da Nazarin Ci Gaba, Iragbiji, The Nation ta rahoto Alausa ya ce za ta inganta fasahar noma don bunkasa samar da abinci a Najeriya.

Ministan ya ce:

“Za ta karfafa sabbin dabarun noma, sarrafa amfanin gona, da kirkirar hanyoyin noma masu jure sauyin yanayi don bunkasa samar da abinci."
"Za ta hada ilimin noma da nazarin ci gaban al’umma, don horar da kwararru da za su taimaka wajen magance matsalolin karkara.
"Haka kuma, jami’ar za ta bunkasa kasuwancin noma da horas da dalibai kan sana’o’in da za su iya dogaro da kai."

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a fusata, sun ta aika kakkausan sako ga gwamnatin Tinubu

A cewar Alausa, jami’ar za ta inganta tattalin arzikin Iragbiji da kewaye, ta hanyar samar da ayyukan yi da bunkasa kasuwanci.

Tinubu ya ki amincewa a kafa jami'a a Adamawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙi amincewa da dokar kafa sabuwar jami’ar ilmi ta tarayya a garin Numan da ke jihar Adamawa.

Wannan mataki na nufin cewa ba za a kafa jami’ar ba, duk da shirin da aka tsara don inganta ilimi a yankin, wanda wasu ke ganin zai jawo koma baya a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.