Zargin Tallafawa Boko Haram: Majalisa Ta Gayyaci Ribadu, DSS da NIA, Ndume Ya Fusata
- Majalisar Dattawa ta bukaci shugabannin hukumomin tsaro na NIA da DIA su bayyana a gare ta kan zargin cewa USAID tana ba Boko Haram kudin tallafi
- Daga cikinsu akwai Mallam Nuhu Ribadu da sauran shugabannin hukumomin DSS da NIA da DIA bayan bukatar bincike daga Sanata Ali Ndume
- Sanatoci sun nuna damuwa kan wani bidiyo da ke nuna wani dan majalisar Amurka, Scott Perry, yana zargin USAID da daukar nauyin ayyukan ta’addanci
- Wannan zargi ya zo bayan CDS, Janar Christopher Musa, ya ce kungiyoyin ta’addanci a Najeriya na samun tallafi da horo daga kungiyoyin kasa da kasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta dauki matakin sanin hakikanin gaskiya kan zargin Hukumar USAID da daukar nauyin ta'addanci.
Majalisar ta bukaci NSA, Nuhu Ribadu da shugabannin NIA da DIA su bayyana a gabanta kan zargin cewa USAID tana ba Boko Haram kudin tallafi.

Asali: Facebook
Dan Majalisa ya zargi USAID da tallafawa ta'addanci
Bukatar binciken wannan zargi na cewa USAID da wasu kungiyoyi suna ba Boko Haram tallafi ya biyo bayan korafin Sanata Ali Ndume, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani taro, Scott Perry ya ce kasafin kudin USAID ya hada da kudin da ake aikawa makarantu, wanda ke taimakawa kungiyoyin ta’addanci.
Shi dai Perry dan jam’iyyar Republican ne, kuma wasu suna zargin Shugaba Trump da kokarin dakile ayyukan USAID.
A watan Janairu, Donald Trump ya dakatar da duk wani taimakon kasashen waje na tsawon kwanaki 90 domin duba ko yana amfani da bukatun Amurka.
Sanata Ndume ya bukaci binciken zargin USAID
Sanatoci sun nuna damuwa kan bidiyon da ke nuna Scott Perry, wani dan majalisar Amurka, yana zargin USAID da daukar nauyin ta’addanci, The Nation ta ruwaito.
Sanata Ali Ndume ya ce wannan zargi ya zo bayan CDS, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa kungiyoyin ta’addanci suna samun horo daga kasa da kasa.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta fara kokarin kawar da kungiyoyi masu alaka da ta'addanci a jihar
Ribadu ya caccaki kasar Canada kan 'visa'
Kun ji cewa Mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya soki gwamnatin Canada kan dakile hafsan tsaro, Christopher Musa shiga kasar.
An gayyaci Janar Musa da tawagarsa zuwa taron girmamawa ga tsofaffin sojoji a Canada, amma wasu ba su samu damar shiga ba.
Mallam Ribadu ya kira hakan da rashin girmamawa, yayin da hafsun ya yi kira ga Najeriya ta tsaya da kafafunta a fagen siyasa ta duniya.
Asali: Legit.ng