Gwamnatin Tarayya Ta Raba N102bn ga Jihohi 28, An Ji Abin da Za Su Yi da Kudin

Gwamnatin Tarayya Ta Raba N102bn ga Jihohi 28, An Ji Abin da Za Su Yi da Kudin

  • Gwamnatin Tarayya ta raba dala miliyan 68.36 ga jihohi 28 a ƙarƙashin shirin SABER, domin inganta kasuwanci da sauƙaƙa saka jari
  • Sakatariyar ma’aikatar kuɗi ta tarayya, ta ce jihohi 33 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar, inda 28 suka karɓi dala miliyan 1 zuwa 4
  • Bankin Duniya ne ke tallafawa shirin SABER wanda ke taimakawa jihohi wajen aiwatar da sauye-sauye, don karfafa ci gaban tattalin arziki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja- Gwamnatin tarayya ta raba dala miliyan 68.36 ga jihohi 28 a ƙarƙashin shirin SABER, wani shiri da Bankin Duniya ke tallafawa don sauƙaƙa kasuwanci a Najeriya.

Babbar sakatariya ta ma’aikatar kuɗi ta tarayya, Lydia Jafiya, ta bayyana haka a taron wayar da kai na ƙasa kan shirin SABER da aka gudanar a birnin Abuja.

Gwamnatin tarayya ta yi magana kan biliyoyin da ta rabawa jihohi 28
Gwamnatin tarayya ta yi bayanin dala miliyan 68.3 da ta rabawa jihohi 28. Hoto: @NGFSecretariat
Asali: Twitter

Jihohi 28 Sun Karɓi Tallafin Daga $1m Zuwa $4m

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nuna tsaurin ido, sun sace shugaba bayan sun harbe shi a Abuja

Lydia Jafiya ta bayyana cewa jihohi 33, ciki har da Abuja, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar karɓar kuɗin, yayin da 28 daga cikinsu suka karɓi tallafin da ya kama daga dala miliyan 1 zuwa miliyan 4.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarta, kudin da aka rabawa jihohi yana daga cikin wani shiri na musamman da ake kira “Prior Results Disbursements,” wanda ke nufin cewa ana bai wa jihohin da suka cika wasu sharudda tallafi.

Ta bayyana cewa, duk da matsalolin da aka fuskanta a farkon shirin, gwamnatocin jihohi sun nuna jajircewa wajen aiwatar da sauye-sauyen kasuwanci don dacewa da ka’idojin shirin.

Amfanin shirin SABER ga jihohin Najeriya

An samar da shirin SABER domin inganta dokokin kasuwanci, rage wahalhalu ga masu saka jari, da ƙarfafa ci gaban tattalin arziki a matakin jiha.

Bincike ya nuna cewa shirin ya taimaka wa jihohi wajen rage matsalolin da ke hana ci gaban kasuwanci, tare da janyo hankalin masu saka jari daga cikin gida da waje.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30

Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin jihohin da suka fi amfana da shirin sun fara aiwatar da sabbin tsare-tsare domin sauƙaƙa rajistar kasuwanci da rage haraji.

Jami'ar ma’aikatar kuɗin ta ce shirin na SABER zai ci gaba da samar da tallafi ga jihohi masu kokari wajen cike ƙa’idojin ci gaban kasuwanci.

'Gwwamnatocin jihohi sun nuna jajircewa' - Lydia

Lydia Jafiya ta ƙara da cewa an tsara shirin ne domin tabbatar da daidaito a rabon kuɗaɗe, tare da bai wa jihohi damar inganta tattalin arzikinsu.

Sakatariyar ta bayyana cewa, duk da matsalolin da aka fuskanta a farkon shirin, gwamnatocin jihohi sun nuna jajircewa wajen aiwatar da sauye-sauyen kasuwanci.

“Bayan jihohi uku kacal, sauran jihohi 33 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar, kuma an raba dala miliyan 68.36 ga jihohi 28 da suka cancanta.”

- Lydia Jafiya.

Tinubu ya yiwa jihohi 34 yayyafin kudi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamnatin Bola Tinubu ta raba N438 biliyan ga jihohi 34 da FCT don rage matsin tattalin arziki.

An fitar da kudin ne a ƙarƙashin shirin NG-CARES bayan tantance jihohin a watan Janairun 2024, kuma an saki kudin kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.