'Yan Bindigar da Ake Zargi da Kisan Ɗan Majalisa Sun Tsere daga Hannun Ƴan Sanda

'Yan Bindigar da Ake Zargi da Kisan Ɗan Majalisa Sun Tsere daga Hannun Ƴan Sanda

  • Wasu da ake zargi da kisan dan majalisa sun tsere daga hannun ‘yan sanda yayin da ake gudanar da bincike kan laifuffukansu
  • Kwamishinan ‘yan sandan Anambra, CP Ikioye Orutugu, ya tura jami’ai don kamo su tare da umartar a ladabtar da duk jami’in da ya yi sakaci
  • An ce an kama wasu da ake zargi da sayen kayayyakin sata tare da kwato motocin da aka yi amfani da su wajen kashe dan majalisar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Wasu da ake zargi da kisan Hon. Justice Azuka, dan majalisa mai wakiltar mazabar Onitsha 1 a majalisar Anambra, sun tsere daga hannun ‘yan sanda.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Awka, babban birnin jihar, a ranar Talata.

Kara karanta wannan

'Ya aikata laifuffuka 5': An gurfanar da fitaccen mawakin Najeriya a gaban kotu

'Yan sanda sun yi magana kan tserewar wadanda ake zargi da kisan dan majalisar Anambra
Wadanda ake zargi da kashe dan majalisar Anambra sun tsere daga hannun 'yan sanda. Hoto: @PPROZONE13UKPO
Asali: Facebook

Wadanda ake zargin sun kashe dan majalisa sun tsere

SP Ikenga ya ce kwamishinan ‘yan sanda, CP Ikioye Orutugu, ya dauki matakan gaggawa don kamo mutanen da suka tsere, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan tserewar wadanda ake zargi, kwamishinan ya kuma umarci a gudanar da bincike tare da ladabtar da duk jami’in da aka samu da sakaci a lamarin.

Binciken farko ya nuna cewa wadanda suka tsere suna taimakawa ‘yan sanda wajen kama wanda ake zargin yana sayen kayayyakin sata da kuma gano motocin da ake amfani da su wajen aikata laifuka.

Yadda wadanda ake zargin suka tsere

A cewar SP Ikenga, yayin aikin damke wanda ake zargin, an samu nasarar cafke mutumin tare da kwato motocin da ake zargi an sace daga jama’a.

Sai dai, yayin wannan samame, mutanen biyu da ake zargi da kisan dan majalisar sun samu damar tserewa daga hannun jami’an da ke rike da su.

Kara karanta wannan

'Abin ya yi muni': An kashe mutane 6 da magoya bayan APC, PDP suka kacame da fada

'Yan sanda sun fara farautar 'yan bindigar da suka kashe dan majalisa
'Yan sanda sun yi sakaci wadanda ake zargi da kisan dan majalisa sun tsere. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Kwamishinan ‘yan sanda ya bayyana cewa tuni rundunar ta baza jami’anta da na leƙen asiri domin tabbatar da cewa an kamo wadanda suka tsere.

Za a hukunta 'yan sandan da suka yi sakaci

Ya tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda tana aiki ba dare ba rana don ganin wadanda suka tsere sun dawo hannun hukuma don gurfanar da su.

Baya ga haka, kwamishinan ya ba da tabbacin cewa duk jami’in da aka samu da laifin sakaci wajen tsaron wadanda ake zargi zai fuskanci hukunci.

Ya ce rundunar ‘yan sandan jihar ba za ta lamunci wani nau’i na gazawa ko sakaci ba, musamman a irin wannan lamari mai matukar muhimmanci.

An gano gawar dan majalisar da aka sace

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe ɗan majalisar jihar Anambra, Hon. Justice Azuka, bayan sace shi a watan Disambar 2024.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun ayyana neman fitaccen mawaki ruwa a jallo, sun gargadi al'umma

Jami’an tsaron haɗin gwiwa da ke bincike kan lamarin sun gano gawar marigayi, Hon. Justice Azuka a gadar Neja ta 2 cikin wani yanayi na ban tsoro.

Bayan makonni ana bincike, jami’an tsaron da aka turo daga Abuja sun cafke wasu da ake zargi da hannu a sace shi a daren Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.