'Yan Bindiga Sun Farmaki Malamin Addini, Sun Kashe Ɗansa da Sace Matarsa
- ‘Yan bindiga sun kashe ɗan faston cocin RCCG kuma sun yi garkuwa da matarsa a tare da neman N30m matsayin kudin fansa
- Faston Austin Ifeji ya tsira bayan an sare shi da adda amma sun kashe dansa yayin da yake ƙoƙarin kare mahaifiyarsa daga 'yan bindigar
- Sai dai, rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta shaida cewa ba ta da masaniya kan lamarin a lokacin da aka tambaye ta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Nasarawa - 'Yan bindiga sun kashe ɗan wani fasto na cocin RCCG, kuma sun yi garkuwa da matarsa a Mararaba, jihar Nasarawa.
An rahoto cewa 'yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari gidan faston, Austin Ifeji, da sanyin safiyar Litinin a Gwagwalada, Mararaba.

Asali: Twitter
Nasarawa: 'Yan bindiga sun kashe ɗan fasto
Bayan an sare shi da adda, Ifeji ya samu nasarar tserewa. Wannan yasa ‘yan bindigar suka yi garkuwa da matarsa domin neman kudin fansa, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokacin harin, ɗansa ya yi ƙoƙarin kare mahaifiyarsa, amma ‘yan bindigar suka harbe shi sannan suka ci gaba da sarar shi da adda.
Wani makwabci, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce bayan kashe yaron, sai ‘yan bindigar suka tafi da mahaifiyarsa, sannan suka nemi N30m kudin fansa.
Rundunar 'yan sanda ta magantu kan harin
Rahotanni sun nuna cewa an yi kokarin ceto yaron a asibiti, amma duk yunkurin da likitocin suka yi ya ci tura.
“Shi ne kaɗai namijin da iyayensa suka haifa, yana da ‘yan mata huɗu. Bai ji daɗin yadda aka muzanta mahaifiyarsa ba, wanda ya sa ya fusata,” inji wata majiya.

Asali: Twitter
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, SP Rahman Nansel, ya bayyana cewa rundunar ba ta da masaniya kan lamarin a lokacin da aka tuntube su.
Wannan harin dai ya kara jefa tsoro a zukakatan mutane, la'akari da karuwar hare-haren 'yan bindiga a garuruwan da ke makotaka da birnin tarayya Abuja.
Mazauna wadannan garuruwa na ci gaba da yin magiya ga jami'an tsaro da su dauki matakan da suka dace na kare rayuka da dukiyoyinsu daga 'yan ta'adda.
Duba wasu labarai kan hare-haren 'yan bindiga
'Yan bindiga sun yi awon gaba da limamin cocin Katolika a jihar Rivers
'Yan fashi da makami sun hallaka wani malamin addinin Kirista a jihar Gombe
'Yan bindiga sun sace malamin addini da matarsa a harin da suka kai Ondo
'Yan bindiga sun kashe babban malamin addinin Musulunci a jihar Kwara
Tsohon ministan Najeriya, Clark ya rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon ministan yaɗa labarai kuma jagoran 'yan Neja Delta, Edwin Clark, ya rasu yana da shekaru 97.
Farfesa C. C. Clark, a madadin iyalan marigayin, ya fitar da sanarwar rasuwar Edwin Clark a daren Litinin, 17 ga Fabrairu, 2025.
An ce rasuwar Edwin Clark na zuwa ne kwanaki kadan bayan mutuwar jagoran kabilar Afenifere, Ayo Adebanjo, wanda ya rasu yana da shekaru 96.
Asali: Legit.ng