Dattawan Arewa Sun Yaba Shirin Tinubu Kan Arewa, Sun Tura Muhimmin Sako ga Gwamnoni

Dattawan Arewa Sun Yaba Shirin Tinubu Kan Arewa, Sun Tura Muhimmin Sako ga Gwamnoni

  • Kungiyar Arewa consultative forum ta bayyana jin dadin yadda shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da hukumomin raya yankin
  • Shugaban ACF, Alhaji Mamman Osuman ya bayyana cewa matakin zai taimaka wajen farfado da yankin da samar da ci gaba mai dore wa
  • Ya kara da tunatar da gwamnonin Arewa 19 halin da jama'arsu ke ciki, da kuma bukatar aiki tare wajen cimma muradun da aka sanya a gaba tare

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar GombeKungiyar 'Arewa Consultative Forum' (ACF) ta yaba wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu bisa kafa Hukumar Ci Gaban Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Shugaban ACF, Alhaji Mamman Osuman, ne ya bayyana hakan a Gombe yayin wata ziyara ga Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya (NSGF).

Kara karanta wannan

"Tinubu sai ya zarce": Matawalle ya yi martani ga jami'in gwamnatin Buhari

Tinubu
ACF ta nemi a farfado da Arewa Hoto" Ismaila Uba Misilli/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Alhaji Osuman ya jaddada cewa sababbin hukumomin za su taimaka wajen rage talauci, da inganta ababen more rayuwa da jin dadin jama’a a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ACF: “Hukumomin ci gaban Arewa za su taimaka”

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Osuman ya kwatanta sabbin hukumomin da Kamfanin Ci Gaban Sabuwar Najeriya da aka kafa a shekarar 1949.

Ya kara da cewa hukumomin za su bunkasa kasuwanci da masana’antu a Arewa, musamman idan aka yi amfani da su yadda ya dace.

Osuman ya gargadi cewa cusa siyasa cikin ayyukan hukumomin na iya hana su cimma manufarsu.

Ya ce:

“Dole a rika nada shugabannin hukumomin ne bisa cancanta, domin a kare mutuncin wadannan tsare-tsare na ci gaban Arewa.”

Ya bukaci hadin kai tsakanin gwamnatocin Arewa da al’ummar yankin domin shawo kan matsalolin da ke addabar yankin.

Kara karanta wannan

Shugabannin Arewa sun yiwa Ganduje kaca kaca, sun kalubalanci tazarcen Tinubu

ACF na son a farfado da Arewa

A jawabinsa, Shugaban kwamitin amintattu na ACF, Alhaji Bashir Dalhatu, ya goyi bayan bukatar daukar matakin hadin gwiwa tsakanin jihohin Arewa.

Alhaji Dalhatu ya jaddada bukatar dawo da martabar Arewa da ta rasa tsawon shekaru, yana mai cewa dole shugabanni da su mayar da hankali kan matsalolin da ke addabar yankin domin inganta rayuwar jama’a.

Ya ce:

“Abu mafi muhimmanci shi ne fahimtar wahalhalun da jama’a ke fuskanta.”

Dalhatu ya bukaci mahukunta su dauki matakan rage radadin da jama’ar Arewa ke ciki cikin gaggawa.

Shirin gwamnoni kan Arewa

A nasa bangaren, Gwamna Inuwa Yahaya ya tabbatar da cewa gwamnonin Arewa guda 19 sun kuduri aniyar magance matsalolin yankin.

Ya jaddada cewa Arewa na da wadatattun albarkatu da za su iya ciyar da yankin gaba, ya kuma yi alkawarin cewa gwamnonin ba za su gaza ba wajen daukar matakan da suka dace domin ci gaban yankin.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima: "Arewa na fama da matsanancin talauci"

ACF ta yi tir da kalaman Ganduje

A baya, mun ruwaito cewa ACF da wasu fitattun ‘yan siyasar yankin sun yi Allah-wadai da kalaman shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, kan tazarcen shugaban kasa.

Abdullahi Ganduje ya bukaci ‘yan siyasar Arewa da ke da burin takarar shugabancin kasa a 2027 su janye, yana mai cewa dole ne a ba Shugaba Bola Tinubu damar kammala wa’adi biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.