'Kafin Rana Ya Fadi': Malamin Musulunci Ya Fadi 'Dalilan' da Za Su Kada Tinubu a 2027

'Kafin Rana Ya Fadi': Malamin Musulunci Ya Fadi 'Dalilan' da Za Su Kada Tinubu a 2027

  • Sheikh Murtala Bello Asada ya ce zai yi wahala Tinubu ya tsallake zabe a 2027, yana danganta hakan da yadda ya nakasa Arewa
  • A cewar Sheikh Asada, matsalolin tsaro, cire tallafi, da kakaba haraji za su taimaka wajen faduwar Tinubu a zaben 2027
  • Ya kara da cewa tsadar rayuwa da yadda ake nuna wa Arewa wariya za su taimaka wajen saukar da gwamnatin Tinubu kafin karfe 12 na rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Sokoto - Sheikh Murtala Bello Asada da ke jihar Sokoto ya sake magana kan zaben Bola Tinubu a shekarar 2027.

Sheikh Asada ya ce zai yi wahala Tinubu ya wuce ƙarfe 12.00 na rana bai fadi ba saboda yadda ya nakasa Arewa.

Malamin Musulunci ya fadi abin da zai kifar da Tinubu a 2027
Sheikh Murtala Bello Asada ya ce kafin 12.00 na rana Tinubu ya fadi a zaben 2027. Hoto: Malam Murtala Bello Asada, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Sheikh Asada ya jero dalilan kwace mulkin Tinubu

Kara karanta wannan

'Arewa ba za ta yafe ba': An fadi yadda Tinubu zai lallabi yankin a zaben 2027

Sheikh Asada ya fadi haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Asabar 15 ga watan Janairun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehin malamin ya yi rubutu a saman bidiyon inda ya jero manyan dalilai da za su nakasa Tinubu a zaben 2027.

Daga cikin matsalolin da Sheikh Bello Asada ya ce za su kifar da Tinubu a zaben sun hada rashin tsaro da cire tallafi da kakaba haraji.

2027: Hujjojin Sheikh Asada domin kada Tinubu

"In shaa Allahu ranar zaɓe a 2027 ko da 12:00 na rana ba za ta yi, wannan azzalumar gwamnati ta faɗi.
"Saboda dalilai kamar haka:
"Wasu manya da suka ɗaure wa ƴan ta'adda gindi ta hanyar hana a kashe su da ƙoƙarin yi musu mafita da sunan sulhu.
"Cire tallafin man fetur don biyan buƙatar kansu.
"Ƙaƙaba wa mutane haraji da ƙarfi, kuma duk wani mai mutunci ya fito ya yi magana amma Bola Tinubu ya fito ya ce babu gudu babu ja da baya.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa Tinubu zai ci zaben 2027': Kwankwaso ya magantu, ya tabo maganar Ganduje

"Tsadar rayuwa wadda ba'a taɓa ganin irin ta ba a tarihi.
"Mayar da mutanen Arewa kamar bayi tare da ɗaukar wasu marasa kishi da nufin kassara mutanen yankin."

Sheikh Asada ya musanta kisan ɗan Bello Turji

A baya, kun ji cewa malamin Musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada ya yi magana kan labarin kisan ɗan Bello Turji da ake yaɗawa.

Malamin ya musanta rahoton da ke cewa an kashe dan Bello Turji inda ya ce ba gaskiya ba ne, ya ce yana raye kuma yana cikin yankin Bawa a bakin iyakar Niger.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.