Najeriya Ta Shirya Dakile Barazanar Trump, Za a Dauki Ma'aikatan Lafiya 28,000 Aiki
- Najeriya ta shirya daukar ma’aikatan lafiya 28,000 da USAID ke daukar nauyi, bayan dakatar da shirin da Amurka ta yi
- Ministan Lafiya ya ce Najeriya na kokarin rage dogaro da tallafin kasashen waje, tare da karfafa bangaren kiwon lafiyar kasar nan
- Dakatar da USAID da PEPFAR na iya shafar yaki da HIV/AIDS, Tarin Fuka da Malaria a Najeriya, amma gwamnati na neman mafita
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin Najeriya ta bayyana shirin daukar ma’aikatan lafiya 28,000 da ke karbar albashi daga hukumar USAID kafin Amurka ta dakatar da ayyukanta.
Ministan lafiya da jin kai, Muhammad Pate, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na kokarin daukarsu aiki domin magance rashin aiki da inganta kiwon lafiya.

Asali: Getty Images
Gwamnati za ta ba ma'aikatan lafiya 28,000 aiki
A zantawarsa da Channels TV, Dakta Pate ya yaba da tallafin Amurka kan kiwon lafiya, musamman kan cututtuka kamar HIV, Tarin Fuka, da Malaria.

Kara karanta wannan
Tinubu zai kinkimo bashin $300m daga Bankin Duniya, an ji abin da zai yi da kudin
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai ya jaddada cewa gwamnatin Bola Tinubu tana da burin karfafa harkar lafiyar Najeriya ba tare da dogaro da tallafin kasashen waje ba.
Ministan lafiyar ya ce:
"Ma’aikatan lafiyar nan 28,000 ‘yan Najeriya ne. Dole ne mu nemo hanyoyin da za mu ci gaba da daukar nauyinsu."
Najeriya ta fuskanci barazanar Trump`
Baya ga dakatar da USAID, shugaba Donald Trump ya kuma toshe shirin PEPFAR wanda ke yaki da cutar HIV/AIDS a duniya.
Hukumar USAID ta dade tana bayar da tallafi ga Najeriya, wanda dakatarwar na iya shafar fannin kiwon lafiya da sauran shirye-shiryen ci gaba a kasar.
Gwamnatin Bola Tinubu na fatan tabbatar da cewa wadannan ma’aikata ba su rasa ayyukansu ba, tare da ci gaba da inganta kiwon lafiyar kasar.
Tinubu ya amince a dauki likitoci 150 aiki
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya amince a dauki likitoci 50 da malaman jinya 100 aiki don inganta kiwon lafiya a gidajen gyaran hali.
Gwamnatin tarayya ta ce za a tura likitocin hukumar NYSC zuwa gidajen kaso domin kula da lafiyar fursunoni da kuma tabbatar da kare hakkinsu.
Asali: Legit.ng