Ramadan 2025: Limaman Yarbawa a Najeriya Sun Sanar da Ranar Fara Azumi
- Kungiyar Limamai da Alfa a yankin Yarbawa, Edo da Delta ta bayyana ranar da za a fara azumin Ramadan na shekarar 2025
- Sanarwar daga ofishin Babban Mufti na Yarbawa ta tabbatar da cewa za a fara azumi daga ranar Asabar, 1 ga watan Maris, 2025
- Kungiyar ta ce sanarwar ta zama al’adar da take yi tsawon shekaru, kuma an yanke shawarar ne bayan jerin taruka da shugabanninta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Kungiyar Limamai da Alfa a yankin Yarbawa, Edo da Delta ta sanar da cewa za a fara azumin Ramadan na 2025 a ranar Asabar, 1 ga Maris.
Sanarwar ta fito ne daga ofishin Babban Mufti na Yarbawa, kamar yadda kungiyar ta bayyana a wata takarda da aka fitar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan
Mawaki ya bijirewa mahaifiyarsa, ya koma soyayya da yar majalisa duk da gargadinta

Asali: Getty Images
Yarbawa sun fadi ranar fara azumin 2025
Rahoton Rabitah na shekarar 1446 AH (2025) ya tabbatar da cewa sanarwar fara azumin an yi ta ne bisa shawarwari da jagorancin shugabannin kungiyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar mai taken "Sanarwa kan Fara Azumin Ramadan" ta fito ne daga taron da aka gudanar a Ibadan, hedkwatar kungiyar Raabitatul Aima Wal Hulamoh.
Kungiyar ta bayyana cewa an cimma matsaya kan ranar fara azumi bayan jerin tattaunawa da shuwagabanni da masana a harkar addini.
Ramadan: An ji ranar fara sallar Tarawihi
Haka nan, kungiyar ta sanar da cewa za a fara sallar Tarawihi daga ranar Juma’a, 28 ga Fabrairu, yayin da za a fara azumi washegari.
Takardar sanarwar ta jaddada cewa wannan tsari yana daidaito da kaso 98 cikin 100 na al’ummar Musulmi a duniya.
Kungiyar ta bayyana cewa fitar da irin wannan sanarwa kafin Ramadan ya kasance al’adar da take aiwatarwa tsawon shekaru da dama.
Karanta sanarwar a kasa:
Gwamnan Jigawa zai ciyar da mabukata a Ramadan
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Jigawa za ta ciyar da mabukata 189,000 a Ramadanan 2025 tare da kashe N4.8bn domin aiwatar da shirin.
A cewar Kwamishinan Watsa Labarai, za a samar da nau'ikan abinci uku a cibiyoyi 630, kowacce cibiya za ta ciyar da mutum 300.
Asali: Legit.ng