Saurari bambanci dake tsakanin sallar Tarawihi da sallar Tahajjud daga bakin Sheikh Jafar

Saurari bambanci dake tsakanin sallar Tarawihi da sallar Tahajjud daga bakin Sheikh Jafar

Da yake muna cikin wata mai alfarma, wata azumin Ramadana, Legit.ng ta dage wajen kawo muku rahotanni masu alaka da azumi, mai azumi da kuma hukunce hukunce hakan a addinin Musulunci, don masu karatu su karu.

Anan ma mun kawo muku wata fatawace da shahararren Malamin addinin Musulunci, marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam ya bayar a zamanin da yake raye game da wata tambaya da aka yi masa dake cewa “Menene bambanci tsakanin Taraweeh da Tahajjud.?”

KU KARANTA: Bari yaro bari: Yaron El-Rufai da jikar Isiyaku sun yi kaca kaca da juna

Shehin Malamin yace babu wani bambanci dake tsakanin sallar Tahajjud da sallar Taraweeh, inda yace dukkaninsu suna nufin abu daya, wato sallar Dare wanda ake yinsu bayan sallar Isha’I kafin ketowar alfijir.

Malam ya kara da cewa: “Sai dai galibi Tahajjud ta fi nuna ma’anar sai da aka yi barci aka farka sa’annan aka yi ta, kamar yadda aya na 79 na suratul Isra’I ta nuna.”.

Sai dai Malam ya tabbarar musatahabbancin bin limami a yayin sallar Tahajjud a cikin Azumi, inda yace an fi so Musulmi ya bi jam’I a watan Azumi a yayin sallar Tahajjud, amma a wajen Azumi an fi so ya yi sallarsa shi kadai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel