Bayan Kashe Mayaka 31, ISWAP Ta Karo Makamai Za Ta Gwabza da Boko Haram

Bayan Kashe Mayaka 31, ISWAP Ta Karo Makamai Za Ta Gwabza da Boko Haram

  • Mayakan Boko Haram sun kai hari kan sansanonin ISWAP a Abadam, Jihar Borno, inda suka yi musu mummunan kisan gilla
  • ISWAP ta karɓi sababbin makamai ta jiragen ruwa biyu daga tafkin Chadi domin shirin ramuwar gayya kan Boko Haram
  • Rikicin na kara tsananta, inda aka samu asarar manyan kwamandojin ISWAP da kuma shirin sake kai farmaki a tsakaninsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Fada mai tsanani ya barke tsakanin ‘yan ta’addan Boko Haram da na ISWAP a Jihar Borno, lamarin da ya janyo asarar rayuka da dama.

Rikici ya samo asali ne bayan da mayakan Boko Haram da ke karkashin jagorancin Bakoura suka kai farmaki a sansanonin ISWAP da ke karamar hukumar Abadam.

Jihar Borno
Boko Haram da ISWAP za su kara gwabza fada. Hoto: Legit
Asali: Original

Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya wallafa bidiyon yadda 'yan ta'addar ISWAP suka karbi makamai a tafkin Chadi a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Bayan zargin masu hannu a ta'addanci, yan ta'adda sun kashe junansu a kazamin hari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa mayakan Boko Haram sun kwace makamai da kayayyakin yaki daga hannun ISWAP, tare da hallaka jagororin kungiyar masu yawa.

A halin da ake ciki, ISWAP ta karbi sababbin makamai domin shirin sake kai hari kan Boko Haram.

Yadda Boko Haram ta kashe ISWAP

A ranar Juma’a, 14 ga watan Fabrairu, mayakan Boko Haram sun kai farmaki kan sansanonin ISWAP da ke yankunan Toumbun Gini da Toumbun Ali a karamar hukumar Abadam.

Wata majiya mai tushe ya shaida cewa mayakan Boko Haram sun afkawa sansanonin ISWAP, inda suka fafata da juna a ranar.

A cewar majiyar, Boko Haram ta kashe jagororin ISWAP da dama, musamman wadanda suka fito daga kabilar Buduma.

Daya daga cikin manyan mayakan da aka kashe shi ne wanda aka ce yana da hannu a kisan manoma sama da 60 a Kukawa a watan Janairu.

Wani daga cikin majiyoyin ya ce:

Kara karanta wannan

An yi kare jini biri jini tsakanin Boko Haram da ISWAP, da dama sun mutu

“Boko Haram sun kashe fiye da ‘yan ISWAP 31, kuma akwai yiyuwar sun fi haka.”

ISWAP ta karbi sababbin makamai

Bayan harin da Boko Haram ta kai, kungiyar ISWAP ta karbi sababbin makamai da kayan yaki ta jiragen ruwa guda biyu da suka shigo daga yankin Kangarwa na Tafkin Chadi.

Mayakan ISWAP sun yi harbe-harbe domin nuna shirin su na mayar da martani ga Boko Haram. Kuma sun gudanar da addu’o’i suna rokon samun nasara a yakin da ke tafe.

Wannan na nuni da cewa ISWAP na shirin yin ramuwar gayya, inda suke kara karfi don sake fafatawa da Boko Haram.

Ana sauraron sake barkewar rikici

Bayan nasarar da Boko Haram ta samu a farko, mayakanta da ke tsibirin Boko Haram sun fara tattara jami’an yaki domin sake kai farmaki kan sansanonin ISWAP a Gemu da Malam Karamti.

Bisa ga binciken, ana sa ran fadan zai dauki sabon salo a karamar hukumar Kukawa, inda mayakan Boko Haram ke kara karfi domin fatattakar ISWAP.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Amurka ya fadi hukumar da ke taimaka wa Boko Haram da ta'addanci

Sojoji sun fatattaki 'yan fashi a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun rundunar sojin kasan Najeriya sun kai farmaki kan wasu 'yan fashi da makami a Kaduna.

An ruwaito cewa sojojin sun samu kiran gaggawa ne a lokacin da 'yan fashin suka tare hanya cikin dare suka fara kama mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng