Matawalle ya Tsoma Baki da Canada Ta Wulakanta Najeriya, Ya Fadi Matakin da Za Su Dauka
- Karamin ministan harkokin tsaro, Bello Matawalle ya tsoma baki kan batun hana sojojin Najeriya 'visa' zuwa kasar Canada
- Matawalle ya bukaci a dauki matsaya mai karfi kan kin bai wa shugabannin sojoji damar shiga Canada, yana kiran a yi bincike
- Ya bayyana cewa kin bai wa sojojin 'visa' cin zarafin martabar Najeriya ne, kuma zai iya kawo cikas ga dangantakar kasashen biyu
- Ministan ya nace cewa idan ba a bada dalili mai gamsarwa ba, dole ne Najeriya ta mayar da martani mai karfi kuma tsayayye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Karamin Ministan harkokin tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa dole ne Gwamnatin Tarayya ta dauki “matsaya mai karfi” kan kasar Canada.
Matawalle yana magana ne bayan da kasar Canada ta ki ba Shugaban Hafsan Sojoji, Janar Christopher Musa, da wasu manyan jami’an soji 'visa'.

Kara karanta wannan
'Abin da ya sa Tinubu zai ci zaben 2027': Kwankwaso ya magantu, ya tabo maganar Ganduje

Asali: Facebook
Nuhu Ribadu ya fusata da kasar Canada
Matawalle ya bayyana takaicinsa kan wannan abu, yana mai cewa kin bai wa tawagar 'visa' babban cin zarafi ne ga Najeriya, kamar yadda ma'aikatar tsaro ta wallafa..
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan Malam Nuhu Ribadu ya caccaki Canada kan abin da ta yi wa hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa da wasu sojoji.
Nuhu Ribadu ya nuna damuwa kan matakin gwamnatin Canada inda ya ce abin takaici ne kwarai da gaske da kuma cin zarafi.
Ya kira matakin da rashin girmamawa, yayin da hafsan ya bukaci Najeriya ta tsaya da kafafunta a fagen siyasa na duniya.
Matawalle ya fadi matakin dauka kan lamarin
Tsohon gwamnan Zamfara ya ja hankali cewa irin wannan dabi’a na iya yin illa ga dangantakar kasashen biyu.
A martaninsa, ministan ya bukaci a gudanar da bincike mai zurfi kan dalilan da suka sa aka ki bai wa tawagar 'visa', yana mai cewa dole ne Najeriya ta dauki matakin diflomasiyya mai tsauri.
“Ba za mu zauna shiru ba a gaban irin wannan raini, dole ne mu dauki matsaya mai karfi a diflomasiyya."
- Cewar Bello Matawalle
Nuhu Ribadu ya ja kunnen Naja'atu Muhammad
Mun ba ku labarin cewa Malam Nuhu Ribadu ya gargadi yar gwagwarmaya, Naja'atu Muhammad ta janye kalamanta da ta yi.
Naja'atu ta yi faifan bidiyo ne inda ta ke zargin Nuhu Ribadu ta sukar Bola Tinubu kan cin hanci da yanzu kuma yake tare da shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng