NNPCL Ya Kara Sauke Farashin Man Fetur a Wasu Gidajen Mai

NNPCL Ya Kara Sauke Farashin Man Fetur a Wasu Gidajen Mai

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa kamfanin NNPCL na kasa ya rage farashin litar man fetur a wasu gidajen mai
  • Bincike ya nuna a wasu gidajen man NNPCL da ke Abuja, farashin ya kasance a yadda yake ba tare da an yi sauyi ba
  • Mutane sun nuna farin ciki da sauke farashin, suna fatan za a aiwatar da shi a sauran jihohin Najeriya
  • Wani mai aikin acaba a Gombe ya zantawa Legit halin da ake ciki kan saukar farashin man fetur a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya rage farashin litar man fetur daga N960 zuwa N945 a wasu gidajen man sa da ke Legas.

Wannan mataki ya zo ne bayan karin farashin da aka yi kwanakin baya, wanda ya kai litar man zuwa N960.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya ƙara bayyana da musulmi suka fara shirye shiryen azumin watan Ramadan

NNPCL
NNPCL ya sauke farashin mai a Legas. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

The Cable ta rahoto cewa saukar farashin ya shafi gidajen man NNPC da ke hanyar Idimu da kuma Ago a Okota, yayin da farashin a gidajen man Abuja bai canza ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataki ya biyo bayan rage farashin man da MRS Oil da kuma matatar Dangote suka yi a kwanakin baya, abin da ke nuna yiwuwar ci gaba da rage farashin a gaba.

NNPCL ya rage farashin man fetur a Legas

A cewar rahoton Daily Post, an samu saukar farashin a wasu manyan gidajen man NNPC da ke Legas, musamman a yankunan Idimu da Okota.

Baya ga NNPC, wasu kamfanonin mai kamar MRS sun rage farashin mai a yankin Kudu maso Yamma zuwa N935.

A yankin Arewa kuma farashin ya tsaya a N945, sannan a Gabashin Najeriya an sayar da lita daya a kan N955.

Kara karanta wannan

Dan ta'adda ya yi kokuwa da soja domin kwace bindiga a cikin daji

Sauyin farashin mai a baya-bayan nan

Kafin saukar farashin, NNPCL ya kara farashin man daga N925 zuwa N960 a Legas, lamarin da ya haifar da koke daga masu abubuwan hawa da sauran jama’a.

A ranar 23 ga Disamba, 2024, kamfanin ya rage farashin litar fetur zuwa N925 a Legas da kuma N965 a Abuja, bayan da a baya ana sayar da lita daya a kan N1,025 da N1,040 a Legas da Abuja.

Sabon rage farashin na zuwa ne bayan da matatar Dangote ta rage farashin man daga N950 zuwa N890, abin da ya janyo hasashen cewa ana iya samun karin raguwar farashi a gaba.

Martanin jama’a kan saukar farashin

Mutane da dama sun nuna farin ciki da saukar farashin, suna masu cewa hakan zai rage musu nauyin kashe kudi kan man fetur.

Haka zalika, masu abubuwan hawa sun bukaci gwamnati da ta tabbatar cewa rage farashin man ya kasance na dindindin, domin hakan zai taimaka wajen rage tsadar sufuri da kayan masarufi.

Kara karanta wannan

NNPCL ya shirya hadaka da Rahama Sadau, Adam Zango da jiga jigan Kannywood

Duk da haka, har yanzu akwai matsin lamba daga jama’a kan cewa har yanzu farashin fetur bai kai yadda ake fata ba, suna fatan ragewar za ta kasance ta ainihi ba ta wucin gadi ba.

Legit ta zanta da dan acaba

Wani mai aikin acaba, Yunusa Muhammad ya zantawa Legit cewa babu alamar sauke farashin a gidajen mai na NNPCL a jihar Gombe.

'Har yanzu ba mu shaida ragin ba. Amma tun da na ce sun fara sauke farashin muna fata ya iso mu."

- Dan acaba

Za a karya farashin abinci a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Neja ta dauki matakin karya farashin abinci domin saukakawa al'umma.

Gwamna Umaru Bago da kansa ya bayyana haka inda ya ce karya farashin zai kawo saukin rayuwa ga al'ummar Musulmi a watan Ramadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel