Ana Shirin Kawo Karshen Zubar da Jinin Manoma da Makiyaya a Jigawa

Ana Shirin Kawo Karshen Zubar da Jinin Manoma da Makiyaya a Jigawa

  • Rikicin manoma da makiyaya a Jigawa ya damu gwamnati, wanda ya sa aka kafa kwamitin sasanci domin daina kashe jama'ar jihar
  • Kwamitin Sasanta Rikicin Manoma da Makiyaya a ƙaramar hukumar Gagarawa ya gudanar taro da kusoshin bangarorin biyu domin nemo mafita
  • Sarkin Gumel, Ahmad Sani, ya bayyana cewa za a iya cimma nasarar wanzuwar zaman lafiya idan aka tattauna tare da neman yadda za a kare afkuwar rikici

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa - A yayin da ake yawaita rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar Jigawa, kwamitin sasanta matsalar a ƙaramar hukumar Gagarawa ya ƙara kaimi wajen dawo da zaman lafiya tsakanin bangarorin da ke rikici.

A ranar Alhamis, kwamitin karkashin jagorancin Hakimin Gagarawa kuma Dokajin Gumel, Kabir Usman, ya gudanar da taron sasanta zaman lafiya a garuruwan Zingaran da Jaftar.

Kara karanta wannan

Ana zargin akwai lauje cikin naɗi da aka kama jami'in NIS ɗauke da manyan makamai

Namadi
An yi zaman sulhu tsakanin manoma da makiyaya a Jigawa Hoto: Umar Namadi
Asali: Facebook

Punch News ta ruwaito cewa taron ya haɗa Hausawa manoma da Fulani makiyaya don warware rikice-rikicen da suka daɗe suna addabar juna a yanki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigawa: Ana yawaita rikicin manoma da makiyaya

Daily Post ta wallafa cewa jihar Jigawa na fama da rikice-rikice mai tsanani a tsakanin manoma da makiyaya, musamman a Gagarawa, Guri, Hadejia da wasu sassa na jihar.

Rikicin kan haifar da rasa rayuka, lalata gonaki, da kuma raba mazauna da gidajensu, musamman a lokacin girbin amfanin gona.

Ana son sulhu tsakanin manoma da makiyaya

Da yake magana a wurin taron, Sarkin Gumel, Ahmad Sani, wanda Bala Muhd ya wakilta, ya jaddada muhimmancin zaman lafiya tare da nuna cewa ana iya samun dawwamammen zaman lafiya ne ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna.

Ya ce:

“Nasarar wannan yunkuri na sulhu na dogaro ne da goyon baya da hadin kan dukkan bangarorin da abin ya shafa.”

Hakimin Yalawa, wanda Malam Gambo Bulama ya wakilta, ya bayyana shirin kwamitin a matsayin babban mataki a tafarkin da ya dace.

Kara karanta wannan

Yawan yin jima'i na hana kamuwa da sankarar maraina ga maza? Likita ya magantu

Ya bukaci dukkanin bangarorin Fulani da manoma da su ajiye bambance-bambancensu domin samun zaman lafiya mai dorewa.

A karshen taron, manoma da makiyaya sun yabawa wannan yunkuri na sulhu, inda suka nuna fatansu cewa wannan sabon ƙoƙarin dawo da zaman lafiya zai haifar da fahimta da haɗin kai a yankin.

An kashe mutane 11 a Jigawa

A baya, mun wallafa cewa An shiga wani yanayi mai tayar da hankali a kauyen Gululu, karamar hukumar Jahun, jihar Jigawa, bayan rikicin da ya barke tsakanin Hausawa da Fulani ya yi sanadin mutuwar mutane 11.

Sulaiman Abubakar Jahun, daya daga cikin dattawan Fulani, ya bayyana yadda rikicin ya shafe shi, yana mai cewa ya rasa yara biyar, yayin da aka yi asara gidaje akalla 31 a tsakanin bangarorin biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel