Gwamnatin Tinubu Ta Bayyana Shirinta a kan Ma'aikata a Najeriya
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya tabbatar da kudirin gwamnatinsu wajen inganta jin dadin ma’aikata da ke Najeriya
- Sanata Kashim Shettima ya jaddada cewa daga cikin irin wadannan matakai, akwai kara mafi karancin albashi zuwa N70,000 a wata
- Ya kara cewa Najeriya ta na da yawan matasa masu ilimin fasaha, wanda ke nuna cewa akwai alamun a rayuwarsu za ta kara inganta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya jaddada kudirin gwamnatin Najeriya na ci gaban jin dadin ma’aikata da inganta manufofin tattalin arzikin da kuma sauye-sauyen albashi.
Ya kuma nanata cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya himmatu wajen tabbatar da samun kwadago mai ƙarfi da tsarin inganta rayuwar ma'aikatan kasar nan.

Kara karanta wannan
'Can ta matse musu': Ribadu ya fusata da aka wulakanta hafsan tsaron Najeriya a ketare

Asali: Twitter
Stanley Nkwocha, Mataimaki na Musamman a Fadar Shugaban kasa kan Harkokin Yada Labarai da Sadarwa ne ya bayyana haka a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shettima ya bayyana hakan yayin wata ganawa da tawagar da Shugaban Hukumar Kwadago ta Duniya (ILO), Mr. Gilbert Houngbo, ya jagoranta tare da Ministan Kwadago, Muhammad Dingyadi, a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja.
Shettima ta yabi tsarin ma'aikatan gwamnatin Tinubu
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yaba da karfin ƙungiyoyin kwadago na Najeriya da rawar da suke takawa a ci gaban kasa.
A cewarsa:
“Mu na alfahari da kwadago mai ƙarfi, wanda kwararren dan Najeriya mai kishin kasa ke jagoranta.
"Shugaba Tinubu yana da matuƙar sha’awa kan jin dadin ma’aikatan Najeriya. Mun kara mafi karancin albashi, kuma mafi yawan jihohi sun fara aiwatarwa."
Ya kara da cewa akwai gwamnonin Najeriya da suka kara mafi karancin albashin da ya haura N70,000 da gwamnatin tarayya ta amince da shi.
"Gwamnati na son ci gaban ma'aikata," Shettima
Mataimakin shugaban kasa ya bayyana cewa Najeriya ta na da sauye-sauyen da za su tabbatar da ci gaban ma'aikatan, a lokacin da kasar ke alfahari da yawan mutanenta a duniya.
Ya ce:
“Ɗaga nan zuwa 2050, za mu wuce Amurka wajen zama ƙasa ta uku mafi yawan mutane a duniya. Matsakaicin shekarun haihuwa a Najeriya ya kai 16.9.
"Muna da yawan matasa, amma idan mun ɗauki matakan da suka dace, za mu mayar da shi albarkatun jama’a maimakon wata matsala.”
Shettima ya ce akwai kwarin gwiwa kan matasan Najeriya a nan gaba, ganin yadda su ke da fahimtar fasahar zamani.
Tinubu ya ba da umarnin daukar ma'aikata
A wani labarin, mun ruwaito cewa a Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da daukar likitoci 50 da malaman jinya 100 aiki domin kula da lafiyar fursunoni a da ake tsare a gidajen gyaran hali daban-daban.
Babban mataimaki na musamman ga Ministan Harkokin Gida, Babatunde Alao, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, inda ya ce an dauki matakin ne don inganta lafiyar daurarru.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng