Sojoji Sun Raunata 'Yan Sanda yayin da Suka Daku da Juna, an Ladabtar da Jami'ai
- Rundunar Sojin Saman Najeriya ta bayyana cewa ta dauki mataki kan rikicin da ya faru tsakanin wasu jami’anta da ‘yan sanda a Warri, Jihar Delta
- Jami’in hulda da jama’an sojojin, AVM Olusola Akinboyewa, ya ce an dauki matakan da suka dace don inganta fahimtar juna tsakanin jami’an tsaro
- An tabbatar da cewa an kula da ‘yan sandan da suka jikkata yayin da jami’an tsaron da suka yi hannun riga ke fuskantar hukunci bisa ka’idojin soja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An samu hatsaniya tsakanin jami’an Sojin Saman Najeriya da ‘yan sanda a garin Warri, Jihar Delta, wanda ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a.
Rikicin ya faru ne a ranar Talata, 11 ga Fabrairu, 2025, inda aka samu rahotannin cewa wasu ‘yan sanda sun jikkata yayin da jami’an NAF suka yi hannun riga da su.

Asali: Facebook
A cikin wata sanarwa da rundunar sojojin ta fitar a ranar Alhamis, ta wallafa a Facebook cewa an shawo kan lamarin, tare da daukar matakan da suka dace domin hana sake afkuwarsa a gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kula da wadanda suka jikkata
Bayanai sun nuna cewa ‘yan sandan da suka samu raunuka sakamakon hargitsin sun samu kulawar likitoci.
Haka kuma, jami’an tsaron da suka shiga rikicin sun fara fuskantar matakan ladabtarwa bisa ka’idojin doka na rundunar soji.
A cikin sanarwar da Akinboyewaya fitar, ya ce:
“A matsayin rundunar da ke aiki bisa ƙa’ida da kwarewa,
"NAF na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da kyakkyawan mu’amala da sauran hukumomin tsaro don kare lafiyar al’umma da tsaron kasa.”
Sojojin sama sun dauki mataki kan rikicin
Rundunar tsaron ta tabbatar da cewa tana daukar matakan hana afkuwar irin wannan rikici a nan gaba.
Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X cewa Akinboyewa ya ce:
“Muna kira ga ‘yan kasa da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro goyon baya da fahimta, domin hada hannu wajen samar da zaman lafiya da tsaro a kasa baki daya.”
Haka zalika, rundunar ta jaddada aniyar ta na ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai.
Bukatar hadin kai tsakanin jami'an tsaro
Rikicin da ya faru a Warri ya janyo hankalin jama’a kan bukatar inganta dangantaka tsakanin hukumomin tsaro domin gudun sake samun irin hakan a nan gaba.
Masana harkar tsaro sun jaddada cewa akwai bukatar hukumomin gwamnati su kara karfafa horo da ilimi kan yadda jami’an tsaro za su rika aiki tare ba tare da samun sabani ba.
Bincike ya nuna cewa irin wadannan sabani tsakanin hukumomin tsaro na iya yin illa ga kokarin da ake yi na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya.

Kara karanta wannan
Ana zargin akwai lauje cikin naɗi da aka kama jami'in NIS ɗauke da manyan makamai
Sojoji sun firgita 'yan fashi da makami
A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun firgita wasu 'yan fashi da makami a jihar Kaduna, inda suka tsere.
Rahotanni sun nuna cewa sojoji sun ceto mutanen da 'yan fashin suka tsare a lokacin da suka tare hanyoyi domin zaluntar jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng