Sojoji Sun Gano Barbashen Jirgin Sama da Ya Yi Hatsari a Borno, An Kashe Mutum 75

Sojoji Sun Gano Barbashen Jirgin Sama da Ya Yi Hatsari a Borno, An Kashe Mutum 75

  • Rundunar sojoji ta gano barbashen wani jirgin sama da ya yi hatsari a Borno; an kashe 'yan ta'adda 75 tare da cafke wasu 138
  • Manjo Janar Markus Kangye ya bayyana cewa sojoji sun kwato makamai 104, harsasai 2,639 da danyen man sata na N646m
  • A yankin Neja Delta, sojoji sun kwato lita 497,152 na danyen mai, lita 142,000 na dizil, da lita 4,075 na tataccen fetur, duk na sata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Rundunar sojoji ta ce dakarunta sun gano wasu injinan jirgin sama biyu daga wani wuri da jirgi ya yi hatsari a Borno.

Daga 3 ga Janairu zuwa 13 ga Fabrairun 2025, sojojin sun kashe 'yan ta'adda 75 tare da cafke masu laifi 138 da kuma ceto mutane 46.

Hedikwatar tsaro ta yi magana da sojoji suka gano barbashen jirgin sama da ya yi hatsari a Borno
Borno: Sojoji sun gano barbashen jirgin sama da ya yi hatsari, an kashe 'yan ta'adda 75.
Asali: Twitter

Borno: Sojoji sun kashe 'yan ta'adda 75

Kara karanta wannan

Sojoji sun firgita 'yan fashi da makami da suka tare hanyoyi a jihar Kaduna

Daraktan yada ayyukan tsaro, Manjo Janar Markus Kangye ya bayyana hakan ga manema labarai a hedikwatar tsaro da ke Abuja, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manjo Janar Kangye ya ce:

"Mun samu injinan jirgi biyu daga wani waje da jirgin sama ya yi hatsari, mun samu makaman roka 16 da bindigar bututu daya."

Daraktan ya shaida cewa dakarun sojojin sun cafke mutane 36 da ake zargin suna satar danyen mai tare da kwato man da darajarsa ta kai N646,189,690.00.

A cewarsa, dakarun sojin sun kwato makamai daban daban da suka kai 104, sannan sun kwato harsasai 2,639 a tsakanin lokacin.

Sojoji sun samu nasarori a Neja Delta

A hannu daya kuma, darakarun soji sun kwato lita 497,152 na danyen man sata, da lita 142,000 na haramtaccen man AGO da aka tace da lita 4,075 na fetur a Neja Delta.

Hakazalika, Manjo Janar Kangye ya ce sojoji sun gano tare da lalata wuraren tace mai 164, ramukan boye mai 37, jiragen safarar mai 19 da rumbunan ajiyar kaya 16.

Kara karanta wannan

Dan ta'adda ya yi kokuwa da soja domin kwace bindiga a cikin daji

Sojojin sun kuma gano tare da lalata durom 38 na mai da kuma wasu wuraren tacen mai 42 da aka gina su ba bisa ka'ida ba.

Sauran abubuwan da aka kwato sun hada da; injinan bar ruwa uku, kekuna hudu, babura bakwai, wayoyin salula biyar da motoci uku da dai sauransu.

'Yan ta'adda sun farmaki sojoji a Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan ta'adda sun kai farmaki ga sojoji da fararen hula yayin da ake ɗaukar gawarwakin manoma 40 da aka kashe a Borno.

Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa, bayan harin, sojoji da fararen hula 54, ciki har da mafarauta, jami'an tsaro na ƴan sa-kai, da 'yan CJTF, sun bace.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel